Gaskiyar Dalilin da Yasa Muka Sauya Sheka Zuwa APC, Yan Majalisar PDP a Ribas Sun Magantu

Gaskiyar Dalilin da Yasa Muka Sauya Sheka Zuwa APC, Yan Majalisar PDP a Ribas Sun Magantu

  • Dan majalisar PDP, Enemi Alabo, ya bayyana dalilin da yasa mambobin majalisar dokokin jihar Ribas 27 suka sauya sheka zuwa APC
  • Alabo ya ce rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP da kuma rigingimun shari’a da suka shafi sakataren jam’iyyar ne yasa suka fice daga jam'iyyar
  • Ya ce sashi na 109 na kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa yan majalisar damar sauya sheka zuwa wata jam’iyya a gabar da aka samu rabuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Port Harcourt, Jihar Rivers - Wani dan majalisar dokokin jihar Ribas, Enemi Alabo, ya yi bayanin dalilin da yasa shi da sauran yan majalisa 26 na jam'iyyar PDP suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Duk wani ‘Dan majalisar dokokin da ya koma APC a Ribas ya rasa kujerarsa – PDP

Alabo ya ce rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP ne babban dalilin da ya sa ‘yan majalisar suka koma APC.

Yan majalisar PDP a Ribas sun sauya sheka zuwa APC
Dalilin da Yasa Muka Sauya Sheka Zuwa APC, Yan Majalisar PDP a Ribas Sun Magantu Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Channels TV a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka kan yadda ya kasa samun tattaunawa da sakatariyar PDP saboda rigingimun shari’a da suka shafi sakataren jam’iyyar.

Yan majalisar sun kuma yi nuni da konewar zauren majalisar Ribas da kuma barazanar da ake yi wa yan majalisar.

Alabo ya bayyana cewa, yan majalisar gaba daya ne suka yanke shawarar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC saboda kalubalen da aka ambata.

Ya yi misali da sashi na 109 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya ba da damar sauya sheka daga jam’iyya a inda ake fuskantar rabuwa.

"Mun samu rarrabuwar kawuna a PDP. Muna da kararraki a kotu da suka shafi sakataren jam’iyyar mu. Mun yi kokarin isa sakatariyar jam’iyyarmu, amma ba mu samu damar haka ba, Yanzu haka da muke magana ba zan iya fada maku wanene sakataren jam'iyyata ba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da suka faru gabanin yan Majalisa 27 su sauya sheka daga PDP zuwa APC

"Idan har ba zan iya samun hulda da jam'iyyata ba, to me nake magana akai? Mun shafe makonni yanzu cikin wannan guguwa kuma tun daga lokacin, babu wata magana daga jam’iyyata a matakin kasa. Wace irin jam’iyya ce wannan?”

Alabo ya ci gaba da cewa:

“Jihar Rivers ta kasance cikin labarai. Majalisar ta yi ta fama da matsaloli, an ci zarafin mu; an danne mu sannan kuma an tauye mu.
"An kona zaurenmu, an razanar da mambobinmu. Yan baranda sun kai mummunan hari gidan kakakin majalisa.
"Yanzu haka da nake magana, babu wata magana daga jam’iyyar da na kira jam’iyya ta. Don haka mambobin majalisa 27 ne muka taru muka ce wa kanmu ba za mu iya ci gaba a haka ba.”

Kungiya ta aika sako ga Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu muhimmin saƙo daga ƙungiyar Ijaw National Congress (INC) kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Rikicin siyasar jihar Rivers ya fara ne biyo bayan yunƙurin tsige gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng