Sun Yi Mutuwar Shahada, Tinubu Ya Magantu Kan Harin Bam a Kaduna, Ya Fadi Abu 1 da Ya Fi Damunsa
- Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya sake mika sakon jaje ga wadanda harin bam ya rutsa da su a Tudun Biri da ke Kaduna
- Tinubu ya ce wadanda su ka mutum sun yi shahada inda ya ce sun mutu su na maimaita kalmar shahada
- Shugaban ya bayyana cewa burinsa ba zai taba cika ba har sai ya kawo karshen rashin tsaro a fadin kasar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya bayyana aniyarsa ta kawo karshen rashin tsaro a kasar baki daya.
Tinubu ya ce ba zai taba samun biyan bukata a zuciyarshi ba har sai ya dakile matsalar tsaro a kasar baki daya, cewar The Nation.
Wane sako ya tura ga wadanda su ka mutu a Kaduna?
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Litinin 11 ga watan Disamba a fadar mai Martaba Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi a Maiduguri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma tura sakon jaje ga wadanda su ka rasa rayukansu a Tudun Biri da ke jihar Kaduna inda ya ce sun mutu da kalmar shahada a bakunansu.
Ya kara da cewa duk wanda zai mutu ya na Maulidi to tabbas ya mutu shahidi tun da babu abin da ake karantawa sai shahada.
Wannan bayani na shugaban na zuwa ne bayan kai harin bam kan masu Maulidi da ya hallaka mutane fiye da 100.
Wane tabbaci Tinubu ya bayar?
Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kulawa da wadanda iftila’in rashin tsaro ya shafa a kasar, cewar Daily Post.
Ya ce:
“Wadannan ‘yan Najeriya ne ma su karfin imani a yayin da su ke gargarar mutuwa su na karanta kalmar shahada.
“Mu na rokon Allah ya bai wa iyalansu hakurin rashi da kuma addu’ar ubangiji ya musu rahama.”
A cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar ya bayyana cewa Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da ba da gudunmawa ga wadanda abin ya shafa.
Tinubu ya kadu da harin bam a Kaduna
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya nuna alhini kan mutuwar masu Maulidi a Kaduna.
A yayin harin bam da sojoji su ka yi, akalla mutane fiye da dari ne su ka mutu dalilin harin a kauyen Tudun Biri.
Asali: Legit.ng