Atiku Ya Shiga Jimami Bayan Samun Labarin Mummunan Hadarin da Ya Auku a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Atiku Ya Shiga Jimami Bayan Samun Labarin Mummunan Hadarin da Ya Auku a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

  • Atiku Abubakar ya tura sakon ta’aziyya ga wadanda suka mutu a hadarin hanyar Kaduna zuwa Abuja da ya auku a yau
  • Ya ce wannan babban abin damuwa ne kuma ya yi jimami, yana mai bayyana halin da ya shiga bayan samun labarin hadarin
  • Ana yawan samun haduran kan titi da ke cinye rayukan mutane da dama, wanda ke jawo dar-dar a hanyoyi a fadin kasar

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana jimami da fadawa radadi kan mutuwar jama’a a Kaduna.

Wannan na zuwa ne bayan da aka ruwaito mutuwar mutane 16 da suka yi hadari a hanyar Kaduna zuwa Abuja, wasu 27 suka jikkata.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Da yake bayyana ta’aziyyarsa, ya bayyana radadin da ya shiga bayan samun labarin mutuwar, ya ce wannan lamari ne mai bukatar tausayawa.

Atiku ya ce ya kadu da jin an yi hadari a Kaduna
Atiku ya yi martani kan abin da ya faru a titin Kaduna zuwa Abuja | Hoto: @atiku
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta’aziyyar Atiku ga ahalin wadanda suka mutu

Da yake mika ta’aziyya da jaje, Atiku ya yada a Twitter cewa:

“Ina matukar bakin ciki da jin mummunan hatsarin da ya afku a yau a kauyen Audu Jhangon da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
“Wannan mummunan al’amari da ya yi sanadin salwantar rayuka 16 tare da raunata mutane 27, babban rashi ne ga al’ummarmu da iyalan da abin ya shafa.
“A wadannan lokuta na jimami, zuciyata ta karkata ga ga dukkan wadanda wannan bala'i ya shafa. Ina mika ta'aziyyata ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu tare da fatan samun warakar gaggawa ga wadanda suka jikkata.
“Ya kamata mu taru a matsayin al'umma don ba da tallafi da mika ta'aziyya ga duk wadanda ke cikin kunci da wadanda ke murmurewa daga wannan lamari mai zafi.”

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kungiyar CAN ta yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna, ta tura bukata

Yadda hadarin ya auku

A tun farko, hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Kaduna ta ce akalla mutum 16 ne suka mutu sannan wasu 27 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamandan shiyyar, Mista Kabir Nadabo, ya ce hatsarin motan ya auku ne a kauyen Audu Jhangon da ke kan titin ranar Abuja zuwa Kaduna a Lahadi, 10 ga watan Disamba, cewar rahoton The Punch.

Ya yi bayanin cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 5:20 na safe, inda wata mota ƙirar DAF mai lamba KUJ 430XC dauke da kaya masu yawa, ta kwace ta fada cikin rami, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.