Dalilin da Yasa Bai Kamata Tinubu Ya Mutu a Ofis Ba, Shahararren Malamin Addini Ya Magantu
- Prophet Abel Boma ya bukaci magoya bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da masu adawa da shi da su taya shi da addu'a
- Prophet Boma ya ce gwanda Shugaba Tinubu ya kammala shekarunsa takwas a mulki da ace mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya maye gurbinsa
- Malamin addinin ya yi hasashen cewa idan Shugaba Tinubu ya yi nasarar jagorantar kasar na shekaru takwasa, "dan kabilar Igbo ne zai gaje shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Prophet Abel Tamunominabo Boma ya bukaci yan Najeriya da su taya Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da addu'a.
Prophet Boma ya bukaci yan Najeriya da su yi wa shugaban kasar addu'a kan jinnu da mutuwar faran daya.
'Lallai kada Tinubu ya mutu": Prophet Boma
Malamin addinin ya bayyana cewa ba zai zama nasara ga abokan hamayyar Shugaban kasa Tinubu ba don shugaban Najeriyan ya mutu a ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boma ya kuma ce idan Tinubu ya kammala wa'adin mulkinsa biyu a 2031, "dan kabilar Igbo zai yi shugabanci".
Ya bayyana a wani bidiyon YouTube na baya-bayan nan cewa:
"Ku yi wa Shugaban kasa Tinubu addu'a. Shugaban kasarmu ne, ku yi masa addu'a. Idan ya mutu, za mu koma baya ne.
"Idan aka bar Tinubu ya kammala wa'adin mulkinsa biyu. Bayan ya yi shugabanci na shekaru takwas, dan kabilar Igbo zai yi shugabanci. Amma idan Kashim Shettima ya karbi mulki, hatta Kudu maso Kudu babu inda za su. Ba zan fada maku abun da Allah bai fada mani ba."
Malamin addini ya yi hasashen 2024
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo a baya cewa Prophet Abel Tamunominabo Boma ya ce akwai makirci da dama a shekarar 2024.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a dandalinsa na YouTube, Prophet Boma ya ce harda Kiristoci cikin masu kulla makircin.
Har ila yau, malamin addinin ya gargadi mutane a kan su yi taka-tsan-tsan a huldarsu da sauran mutane. Da yake ci gaba da jawbai, Prophet Boma ya yi karin wasu hasashe biyu.
Asali: Legit.ng