Sarkin Kano Ya Yi Wata Magana Mai Jan Hankali Kan Tsohon Ministan Sadarwa Sheikh Isa Pantami
- Sarkin Kano ya yabawa tsohon ministan sadarwa, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami inda ya ce kullum sai ya saurari karatunsa
- Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa yana kallon kansa a matsayin ɗalibain Pantami, kuma yana girmama shi
- Sarkin ya yi wannan magana ne a wurin taron kaddamar da wani littafi, wanda tsohon mai ba gwamnan Kano shawara ya rubuta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin ɗaliban Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.
Sarkin ya ce duk da bai taɓa zama a gabansa ya ɗauki karatu ba amma a kowace rana sai saurari katun Sheikh Pantami, tsohon ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani.
Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta
Bayero ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da littafin, "An Introduction to Strategic Communication” wanda Dakta Sule Ya’u Sule ya wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pantami, wanda shi ne shugaban taron ya wallafa hotunansa da mai martaba Sarkin Kano a shafinsa na Facebook ranar Jumu'a, 8 ga watan Satumba, 2023.
Muna girmama Pantami - Sarki
Da yake nasa jawabin a wurin kaddamar littafin, uban taro kuma sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya ce Pantami na ɗaya daga cikin Malaman Musulunci da suke ganin girmansu.
A kalamansa, sarkin ya ce:
"Na saurari jawabi daga mutanen da nake ganin girmansu, mutum na farko shi ne Sheikh Pantami (tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani)."
"A duk lokacin da na haɗu da Pantami, na kan faɗa wa mutane na cewa yana ɗaya daga cikin manyan malaman da muke girmama su a ƙasar nan ta mu."
"Haka nan kuma duk da ban zauna na yi karatu a gabansa ba, ina kallonsa a matsayin malamina domin babu ranar da za a wayi gari har rana ta faɗi ban saurari karatunsa a waya ba."
Haka nan Sarkin ya yaba wa Sardaunan Kano watau tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau, inda ya ce kowa ya san kyakkyawar alaƙarsa da mahaifinsa, marigayi Ado Bayero.
Izala Ta Yi Allah Wadai da Kisan Masu Bikin Maulidi a Kaduna
A wani rahoton kuma Yayin da ake jimamin mutuwar masu Maulidi a Kaduna, kungiyar Izala ta yi martani kan iftila'in da ya faru a ranar Lahadi.
Kungiyar ta yi Allah wadai da wannan mummunan hari inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi kwakkwaran bincike.
Asali: Legit.ng