Tirkashi: Yan Sanda Sun Kama Matashi Yana Lalata Da Zakara a Jihar Adamawa
- An damke Lawali Mori mai shekaru 17 yana lalata da zakara a kauyen Viniklang da ke jihar Adamawa
- An kama matashin ne bayan wata mazauniyar yankin, Esther Dimas ta kama shi yana aikata masha'ar sannan ta kai kara wajen yan sanda
- A cewar yan sanda, matashin ya sanar da cewar ya aikata laifin amma bai fadi dalilansa na aikata hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Adamawa - Rundunar yan sanda ta kama wani matashi dan shekaru 17 mai suna Lawali Mori kan zargin lalata da wani zakara a Viniklang, karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki ta shafin rundunar a dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @AdamawaPoliceNG, a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba.
Nguroje ya bayyana lamarin a matsayin "laifi da bai dace ba".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa an kama Mori ne bayan wata mazauniyar yankin, Esther Dimas ta kama wanda ake zargin yana cikin aikata laifin.
Ya ce:
“An yi kamen ne sakamakon wani korafi da wata Esther Dimas da ke zaune a Viniklang ta kai wa yan sanda, bayan ta kama wanda ake zargin yana cikin aikata laifin. Wanda ake zargin ya kara bayyana cewa yayi lalata da zakara amma ya kasa bada dalilan da yasa yake aikata hakan.
"Sai dai kuma, yayin da yake nuna damuwarsa kan lamarin, kwamishinan yan sanda, CP Afolabi Babatola, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.”
An kama matashin da ya kashe mahaifinsa
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa wani matashi dan shekaru 20, David Felix, ya kashe mahaifinsa kan cewa yana zuwa masa a cikin mafarki.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, matashin ya aikata laifin ne a gidansu da ke kauyen Madakiya, karamar hukumar Zango-Kataf ta jihar Kaduna.
An tattaro cewa Felix ya yi zargin cewa mahaifinsa na zuwa masa a mafarki a matsayin tsuntsu mai dauke da fuskar mutum, yana kokarin cutar da shi, saboda haka bai da wani zabi da ya wuce ya kashe shi.
Asali: Legit.ng