Gwamnan APC ya Sa Ladan Naira Miliyan 50 Ga Duk Wanda Ya Taimaka Aka Kama Makasan Hadiminsa
- Gwamnatin Ogun ta sanya ladan N50m ga duk wanda ya taimaka da bayanan sirri har aka kama makasan daraktan kuɗi
- Kusan mako biyu da suka wuce wasu yan bindiga suka kashe hadimin gwamnan a hanyar komawa ofis, suka sace makudan kuɗi
- Tun bayan lamarin, Gwamna Dapo Abiodun ya sha alwashin tabbatar da an hukunta duk mai hannu a kisan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da cewa zata ba da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka da bayanan da za su kai ga kama wadanda suka kashe Mista Taiwo Oyekanmi.
Gwamnatin ta ce wannan lada zata ba da shi ne ga duk wanda ya kawo bayanan sirri da zasu taimaka har a damke makasan Oyekanni, daraktan kudi a ofishin Gwamna Dapo Abiodun.
Yadda aka kashe hadimin gwamnan
Channels tv ta ce a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023, wasu yan bindiga suka halaka hadimin gwamnan a kan gadar Kuto a Abeokuta, babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce maharan sun biyo marigayin wanda ke tare da wasu jami'an gwamnati biyu a hanyar komawa ofis bayan sun ciro tsabar kuɗi masu yawa daga banki.
Rahoto ya tabbatar da cewa ƴan bindigan sun tare su, sannan suka kashe Akantan na ofishin gwamna, kana suka yi awon gaba da maƙudan kuɗaɗe.
Abiodun ya ɗauki matakin kama yan ta'addan
Gwamna Dapo Abiodun ya bayyana jimaminsa da kisan babban ma'aikacin, inda ya ce lamarin ya gigita gwamnatinsa.
Amma ya lashi takocin cewa zai yi duk mai yiwuwa har sai waɗanda suka kashe hadimin sun zo hannu kuma doka ta yi aiki a kansu.
Sai dai a wata sanarwa da gwamnatin Ogun ta fitar a ranar Juma’a, ta ce tukuicin N50m na jiran duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen kamo ƴan bindigan.
A rahoton Daily Post, sanarwan ta ce:
“Gwamnatin Ogun ta tanadi tukuicin N50m ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kashe daraktan kudi na jiha, Mista Taiwo Oyekanmi, a ranar 30 ga Nuwamba, 2023 a Abeokuta."
"Duk bayanan da mutum ya bayar za a ɗauke su da matuƙar muhimmanci ko a sirri ba tare da kowa ya sani ba."
Sanusi Lamido ya samu giyon baya kan naɗin ministan fetur
A wani rahoton kuma Dattijon kasa kuma tsohon ministan kuɗi ya goyi bayan kalaman tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido kan kujerar ministan man fetur.
Chief Olu Falae ya ce ya kamata a samu wani mai gaskiya ya riƙe muƙamin a madadin shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng