Tsohon Sarki Sanusi Ya Faɗi Gaskiya, Ya Samu Goyon Baya Kan Wanda Ya Dace a Naɗa Ministan Man Fetur

Tsohon Sarki Sanusi Ya Faɗi Gaskiya, Ya Samu Goyon Baya Kan Wanda Ya Dace a Naɗa Ministan Man Fetur

  • Dattijon kasa kuma tsohon ministan kuɗi ya goyi bayan kalaman tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido kan kujerar ministan man fetur
  • Chief Olu Falae ya ce ya kamata a samu wani mai gaskiya ya riƙe muƙamin a madadin shugaban Najeriya
  • Tsohon shugaban ƙaa, Muhammadu Buhari, ya riƙe ministan man fetur har ya sauka daga mulki, Tinubu ya bi layinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wani dattijon ƙasa kuma tsohon ministan kudi, Cif Olu Falae, ya ce ba bu bukatar a ce sai shugaban ƙasa a Najeriya ya riƙe kujerar ministan man fetur.

Ya bayyana cewa abu ne mai matuƙar amfani Shugaban Kasa ya naɗa wani daban a matsayin ministan albarkatun man fetur, wanda Najeriya ke tunƙaho da shi.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi maganar kisan masu Maulidi, ya fadi nasarar farko da aka samu

Sanusi Lamido da shugaba Tinubu.
Tsohon Sarki Sanusi Ya Faɗi Gaskiya, Ya Samu Goyon Baya Kan Wanda Ya Dace a Naɗa Ministan Man Fetur Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Wannan matsaya ta tsohon ministan ta yi daidai da maganar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton The Cable, Sanusi ya ce ba sai shugaban ƙasa ya riƙe ministan man fetur ba, inda a ganinsa naɗa wani daban zai ba da damar tuhumarsa idan al'amura ba su tafi daidai ba.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rike mukamin a lokacin mulkinsa yayin da magajinsa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗora daga inda ya tsaya.

Wa ya kamata a naɗa a matsayin ministan fetur?

Amma dattijon ya ce ya kamata ma’aikatar man fetur ta samu wani mutum daban a matsayin minista ba shugaban kasa ba.

Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin Channels tv ranar Alhamis, Chief Olu Falae ya ce:

Kara karanta wannan

Sanusi Lamido ya caccaki Shugaba Tinubu, ya nemi wani muhimmin abu 1

"A ganina ya kamata a samu minista a kowane ɓangare mai muhimmanci a gwamnati ciki har da man fetur. Na san batun man fetur na da girma wajen samun kuɗin shiga."
"Babu shugaban ƙasan da yake iya tsame hannunsa kacokan daga harkokin fetur banda Babangida saboda muna da ministan man fetur a lokacin, banda Obasanjo saboda akwai Buhari a matsayin ministan fetur."
"Ya zama dole a ce muna da wani mai gaskiya a matsayin ministan da zai tafiyar da harkokin man fetur ta yadda shi za a tuhuma idan an samu matsata."

PDP ta faɗi gaskiya kan batun haɗa maja

A wani rahoton na daban Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa a halin yanzu tana kokarin farfaɗowa bayan kashin da ta sha a zaben shugaban ƙasa na 2023.

Babbar jam'iyyar adawa ta kasa ta faɗi haka ne yayin da take musanta rahoton cewa ta fara shirin haɗa maja da wasu jam'iyyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262