"Himma Ba Ta Ga Rago": Dalibar Najeriya Ta Yi Hijira Zuwa Turai, Ta Kama Aikin Noma Gadan-Gadan

"Himma Ba Ta Ga Rago": Dalibar Najeriya Ta Yi Hijira Zuwa Turai, Ta Kama Aikin Noma Gadan-Gadan

  • Wata yar Najeriya da ta mallaki kwalin digiri wacce kasuwancinta ke tafiya daidai a Najeriya ta siyar da shi sannan ta koma kasar Spain
  • A sabuwar kasar da take zama, abubuwa basu tafi kamar yadda ta yi tsammani ba, inda ta koma aikin noma duk da cewa ta yi digiri
  • Yan Najeriya da dama da suke fuskantar irin haka a kasar waje sun bayyana halin da suke ciki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiya yar Najeriya ta hada hotuna a TikTok don ba da labarin yadda tafiyarta turai ta kasance.

Matashiyar ta ce kafin ta bar kasar, ta siyar da gaba daya kasuwancinta (shago) sannan ta sallami ma’aikatanta.

Kara karanta wannan

"Na gaji da kasar nan": Dirama yayin da yar Najeriya ta nemi kwandastan mota ya kai ta Amurka

Yar Najeriya ta yi balaguro zuwa turai inda ta kama aikin noma
"Himma Ba Ta Ga Rago": Dalibar Najeriya Ta Yi Hijira Zuwa Turai, Ta Kama Aikin Noma Gadan-Gadan Hoto: @seen.thia
Asali: TikTok

Yar Najeriya da ke aikin noma a Spain

Da isarta kasar da take mafarki, matashiyar ta ce wurin yana da matukar kyau sannan ta dunga ji kamar a aljannah take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa sun fara sauyawa ne yayin da take farautar aikin yi kuma bata da zabin da ya wuce fara harkar noma. Hakan yasa abubuwa suka yi mata yawa.

Ta kara da cewar dole ta yasar da satifiket dinta sannan ta kama aikin duk da yadda yake da wahala saboda dole sai ta biya wasu kudade.

Ta kai a zamanta a Spain, sai da ta siyar da wayarta na iPhone don ta samu na gudanar da harkokinta. Ta fuskanci abubuwa da dama kafin abubuwa suka fara daidaita.

Kalli bidiyonta a nan.

Jama’a sun yi martani

Savage Queen ta ce:

Kara karanta wannan

"Sun yi zaton damfara nake yi": Mai aiki a gidan mai ta dau wanka ta bayan aiki, bidiyon ya yadu

“Eh da gaske ne ba za ka iya samun aiki da digirin kasar waje ba sai ka je makaranta a nan sai ka je jami’a digirin waje baya aiki a nan.”

JaidyLiveTv ta ce:

“Wannan ba wani abu bane idan har mutum ya fara zuwa Spain, abubuwa za su daidaita zuwa wani lokaci. Na fara da aikin gona a 2017 yanzu ni farfesan Turnci ne a Madrid. Kada ki dakata.”

Shoner ñïce ta ce:

“Ban san me yasa nake dariya ba a’a! magana ta gaskiya na san dalili, saboda nima abun da nake fsukata kenan a yanzu.”

Beautiful ta ce:

“Wayyo kawata a nan muna tunanin abubuwa sun yi maki daidai a chan.”

Budurwa ta ce ta gaji da Najeriya

A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya ta bukaci wata motar bas ta kai ta Amurka yayin da ta dage cewa ita ta gaji da kasar nan.

Wani bidiyo da ke yawo a TikTok ya nuno lokacin da matashiyar ta tsayar da motar bas sannan ta bukaci a tukata zuwa Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng