Wakilan Gwamnatin Kaduna Sun Dira Garin da Sojoji Suka Kashe Bayin Allah a Taron Maulidi

Wakilan Gwamnatin Kaduna Sun Dira Garin da Sojoji Suka Kashe Bayin Allah a Taron Maulidi

  • Wakilan gwamnatin Kaduna karkashin mataimakiyar gwamna sun kai ziyarar ta'aziyya kauyen Tudun Biri ranar Talata
  • Wannan ya biyo bayan umarnin Gwamna Uba Sani na gudanar da binciki kan harin sojojin da ya kashe bayin Allah a kauyen
  • Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ɗauki laifin cewa jami'anta ne suka yi kuskuren sakin bam a wurin taron Maulidi ranar Lahadi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Tawagar wakilan gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe, sun isa ƙauyen Tudun Biri, ƙaramar hukumar Igabi.

Jami'an gwamnatin Kaduna sun je ta'aziyya Tudun Biri.
Jami'an Gwamnatin Kaduna Sun Dira Kauyen da Sojoji Suka Kashi Bayin Allah Hoto: Salma Musa/Facebook
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa a ƙauyen Tudun Biri ne sojojin Najeriya suka saɓa saiti suka saki bam a wurin taron Maulidi, lamarin da ya yi ajalin mutane sama da 80.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mun yi takaici, shugaban sojoji ya roki afuwa kan kisan mutum 85

Wakilan gwamnatin Kaduna da suka ziyarci ƙauyen sun haɗa da shugaban ma'aikata, Sani Liman Kila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take jawabi ga al'umma, mataimakiyar gwamnan ta ce sun kawo wannan ziyara ne domin jajantawa dangogin waɗanda suka rasu sanadin wannan ibtila'i na ranar Lahadi.

Malam Uba Sani ya ɗauki mataki

Tuni dai Gwamna Malam Uba Sani ya bada umarnin gudanar da bincike kan harin jirgin sojojin wanda ya halaka bayin Allah Musulmai da tsakar dare.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Uba Sani ya ce ya kaɗu matuka da samun labarin lamarin da ya kashe fararen hula da ba ruwansu.

Gwamnan ya ce:

"Na ba da umarnin gaggauta bincike mai zurfi kan mummunan lamari, zamu yi kokarin kare maimaita faruwar irin haka nan gaba kuma ina tabbatar da cewa za a fifita tsare mutane a yaƙin da ake da 'yan ta'adda."

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya ƙara samun gagarumin goyon baya da ka iya sa ya lallasa Abba a Kotun Koli

"Haka nan kuma na bada umarnin a hanzarta maida waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitin Barau Dikko domin a musu magani, gwamnati zata ɗauki nauyin ɗawainiya da su."

Gwamnatin Kaduna ta ce rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ɗauki laifin wannan kuskure, tana mai cewa ba da nufi jami'anta suka jefa bam ɗin ba.

Babban hafsan sojoji ya roƙi afuwar abinda ya faru a Kaduna

A wani rahoton kuma Rundunar sojojin Najeriya ta nemi yafiyar al'ummar Tudun Biri, gwamnatin Kaduna da al'ummar jihar bisa harin bam na ranar Lahadi da ta gabata.

Shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Lagbaja ya nemi yafiyar yayin da ya ziyarci jihar Kaduna don gani da ido kan iftila'in da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: