Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutane 7 a Manyan Muƙaman Hukumar NIS Ta Ƙasa

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutane 7 a Manyan Muƙaman Hukumar NIS Ta Ƙasa

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabuwar shugabar hukumar shige da fice da mataimaka shida
  • A wata sanarwa ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, naɗin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba
  • Adepoju, sabuwar kwanturola janar ta hukumar kwastam ta riƙe muƙamai da dama gabanin zuwa wannan matakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Misis Caroline Wura-Ola Adepoju a matsayin kwanturola janar ta hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS).

A rahoton The Nation, bayan haka Tinubu ya amince da naɗin sabbin mataimakan kwnaturola guda shida kuma naɗin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu ya siya hannun jarin Atiku na $100m a kamfanin Intels? Fadar shugaban kasa ta yi magana

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade Bakwai a Hukumar Kwastam Ta Kasa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sakataren majalisar kula da hukumomin sibil difens, shige da fice, kashe gobara da ta gyaran hali, Alhaji Ahmed Jaafaru, ne ya sanar da haka ranar Litinin, 4 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Gabanin wannan naɗi da aka mata, Misis Adepoju ta riƙe muƙamin mataimakiyar kwanturola Janar (DCG) mai kula da sashin kuɗi kuma ta riƙe mukaddashin CG."

Jerin mataimakan CG guda 6

Jaafaru ya bayyana sunayen waɗanda aka naɗa a matsayin mataimakan shugaban NIS, wanda suka ƙunshi Zainab Lawal, Auna Usman Aliyu, da Nandap Kemi Nannan.

Sauran sun haɗa da Usman Babangida, Hassan Sadat da kuma Emenike Ijeoma Chidi.

Taƙaitaccen tarihin sabuwar shugabar kwastam

Adepoju, wadda ke riƙe da muƙamin CG ta riko tun 1 ga watan Yuni, an haife ta ranar 13 ga watan Yuli, 1963 a ƙaramar hukumar Oluji/Okeigbo, jihar Ondo.

Ta yi makarantar sakandiren mata Christ Girls’ School, Ado Ekiti, inda ta karbi shaidar kammala sakandire WAEC a shekarar 1980.

Kara karanta wannan

Shin Tinubu ne? Atiku ya bayyana wanda ya siyarwa hannun jarinsa na $100m a kamfanin Intels

Haka nan kuma ta yi karatun digiri na farko a sashin koyon ilimin kimiyya na jami'ar Maiduguri, inda ta kammala a 1985, Premium Times ta ruwaito.

A shekarar 1987 ta wuce Jami’ar Ibadan, inda ta samu digiri na biyu a fannin Chemistry. Hakanan tana da takaddun shaida daga Kwalejin Trios Hamilton, Ontario, da Kanada Paralegal Studies.

APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 38 a Ekiti

A wani rahoton kuma Hukumar zaɓe ta jihar Ekiti ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023.

Shugaban hukumar, Cornelius Akintayo, ya ce jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujerun ciyamomi 38 da kansiloli 177.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262