Rake: Mata a Kaduna Sun Koka Da Karanci, Tashin Farashi, Manomi Ya Fada Dalilin Tsadarsa

Rake: Mata a Kaduna Sun Koka Da Karanci, Tashin Farashi, Manomi Ya Fada Dalilin Tsadarsa

  • Mata masu sana'ar siyar da rake sunyi korafi dangane irin wahalar da suke fuskanta don nemo raken kafin su kawo kasuwa ko wurin da suke sayarwa
  • Masu siyar da raken sun yi korafi kan yadda ba a samun isasshiyar riba duk da wahalar da suke sha kafin kawowa kwastomominsu raken
  • Wani manomin rake ya ce tsadar na da nasaba da irin tsadar kayan gona da kuma takin zamani

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Kaduna - Matan da ke sanar'ar siyar da rake a Kulmin Kaduna da ke karamar hukumar Igabi sun bayyana yadda karancin rake ya janyo tashin farashinsa a kasuwa.

Suna yin tafiya a kwale-kwale don nemo rake, tare da bayyana damuwa kan karancin riba.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Sandunan Rake
Mata masu sana'ar sayar da rake a Kaduna sun koka kan karancinsa da tsadar farashi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suna barin gidajensu tun safiya misalin 5 na asuba, don kawai su nemo rake.

Lami Thomas, wata mai siyar da rake, ta bayyana irin kalubalen, in da ta ce suna samun yar karamar riba duk da wahalar da suke sha wajen samo raken.

Victoria Gambo ta bayyana irin wahalar da ake sha, tana mai cewa duk da yadda suke barin 'ya'yansu a gida don kasuwanci, ribar karama ce. Ta na fatan samun yalwar tattalin arziki yadda za a fita daga kangin rashin kudi.

Halima Dogara, wata mai siyar da raken, ta bayyana wahalar da suke sha wajen komawa gida a makare, ta kara da cewa tsadar rake na da nasaba da rashin saka hannun gwamnati, in da ta ce matan kauye ba sa samun tallafi.

Mennene ya haifar da tsadar raken a Kaduna?

Muhammad Mansir, wani manomin rake, ya alakanta tsadar rake da yanayin tsadar taki, fetur da kuma sauran kayan noma.

Kara karanta wannan

Dan shekara 18 ya fadi yadda ya kashe tsohuwar shugabar makaranta bayan sace wayarta a Ondo

Ya ce takin da suke siyan buhu N6,500 zuwa 7,00 amma yanzu N20,000 suke siya.

Ya bukaci gwamnati ta shigo don taimakawa, tallafin takin zamani da rage kudin fetur zai rage tsadar kayan noma ta yadda farashi zai yi kasa a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164