Gwamnatin Tinubu Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Halasta Auren Jinsi a Sirrance? Gaskiya Ya Fito

Gwamnatin Tinubu Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Halasta Auren Jinsi a Sirrance? Gaskiya Ya Fito

  • Rubutun da ke tare da wani bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar halasta auren jinsi
  • Amma batun bai shafi halasta auren jinsi ba, kuma gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta rattaba hannu kansa ba, a cewar rahoton binciken gano gaskiya
  • Legit.ng ya rahoto cewa kasashe fiye da 60 suna da dokokin haramta auren jinsi, fiye da rabinsu kasashen Afirka ne

FCT, Abuja - Wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya yi ikirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta rattaba hannu kan yarjejeniyar halasta auren jinsi a kasar a boye.

Lakabin da ya danganci auren jinsi da masu sauya jinsi, masu sauya jinsi da masu luwadi da madigo.

Tinubu bai halasta auren jinsi ba
Najeriya na da dokar haramta auren jinsi. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Lakabin da aka yi wa bidiyon mai cike da kura-kurai ya ce:

Kara karanta wannan

Ma'aikacin Karamar Hukuma Ya Fadi Matacce a Ofis, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yanzu luwadi da madigo halas ne a Najeriya. An rattaba hannu kansa ne cikin sirri amma na ga alamun yana zuwa.
"Daya daga cikin dalilan da yasa Tinubu ya yarda shine saboda Amurka da Ingila. Ta yi wu wannan yarjejeniya ne domin su amince su halasta gwamnatinsa. Ban san ya Shettima zai ji a ransa ba.
"Ban san yadda musulmi za su ji ba, ban san yadda kiristoci za su ji ba. Ban san ya jihohin da ke Shari'a za su ji ba."

An ga bidiyon a Facebook a nan da kuma nan.

Luwadi, madigo har yanzu halas ne a Najeriya

Ikirarin halasta abin ya saka kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC, ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da yarjejeniyar.

A cikin sanarwar da ta aike wa Legit.ng a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, MURIC ta ce kasashen Yamma karkashin European Union-ACP (Africa, the Caribbean and Pacific (ACP) suna matsawa Najeriya lamba ta shiga cikin kasashen da suka halasta auren yan madigo, luwadi, da masu sauya jinsi.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya raba daloli a unguwa, Kirkinsa ya tsorata mata, sun tsere a bidiyo

Sai dai, kafar binciken gano gaskiya, Africa Check, ya yi bincike kan ikirarin cewa Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar halasta auren jinsi. Za a iya ganin sakamakonsa a kasa:

"Dokar Hana Auren Jinsi na Act 2013, wanda ya fara aiki a 2014, ya hana 'bayyana soyayya a fili tsakanin jinsi iri daya' kuma ya tanadi daurin shekara 14 a gidan yari ga 'duk wanda aka samu ya yi auren jinsi ya aikata laifi kuma za a iya hukunta shi". Har yanzu dokar tana aiki.
"Ikirarin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar halasta auren jinsi a kasar ba gaskiya bane."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164