Ma'aikacin Karamar Hukuma Ya Fadi Matacce a Ofis, Bayanai Sun Fito
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Jihar Ondo - Wani ma'aikaci a Bolorunduro, Karamar Hukumar Ondo ta Gabas a Jihar Ondo, da aka ce sunansa Mathew ya fadi ya mutu a ofishinsa.
Daily Trust ta gano cewa Mathew, wanda ke zaune a garin Elemosi a Ondo, ya fadi nan take ya kuma mutu cikin yan mintuna a ofishinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin, a cewar abokan aikinsa, ya zo ofis a ranar Juma'a sannan daga baya ya tafi ya yi karin kummalo a cikin motansa da ya yi fakin a cikin karamar hukuma.
Daya cikin abokan aikinsa, wanda bai so a ambaci sunansa, ya ce sun yi mamaki bayan Mathew ya dawo ofis ya tarar da sauran abokan aikinsa suna hira amma ya fadi nan take kuma aka gaza farfado da shi.
Ya ce:
"Ba bu alaman rashin lafiya tare da shi. Abin ya bamu mamaki. Mun garzaya da shi asibiti a Bolorunduro amma likitoci sun tabbatar ya mutu. Mutuwarsa ya daure mana kai."
Majiyar Legit Hausa ta yi kokarin ji ta bakin matar mammacin amma hakan bai yi wu ba domin wadanda ke kusa da iyalan sun ce tana jimamin mutuwarsa.
Daya daga cikin majiya daga iyalan, ya bayyana cewa yan uwansa sun fara shirin birne shi.
Da aka tuntube ta, Mrs Funmilayo Odunlami-Omisanya, Mai Magana da yawun rundunar yan sanda (PPRO) a jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin a hirar da aka yi da ita a ranar Asabar.
Ta yi bayanin cewa yan sanda suna bincike kan ainihin abin da ya yi sanadin mutuwar mamacin, ta kara da cewa gawarsa na dakin ajiye gawarwaki na asibitin.
Asali: Legit.ng