Kakakin Majalisar Wakilai Ya Karanto Sunayen Sabbin Shugabannin Kwamitoci 27 da Mataimaka
- Majalisar wakilan tarayya ta yi gyara a shugabancin kwamitoci 27 yayin da aiki ya fara kankama kan kasafin kuɗin 2024
- Tajudeen Abbas ya karanto sabbin ciyamomin kwamitocin da mataimakansu biyo bayan tsige wasu yan majalisa da kotu ta yi
- Ya umarci su gaggauta miƙa ragama ga sabbin domin aikin zama da ma'aikatu da hukumomin gwamnati ya tafi cikin sauƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kakakin majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajuddeen, ya karanta sunayen sabbin shugabannin kwamitoci 27 da mataimakansu na majalisar.
Kwamitocin sun kunshi guda 26 da ake da su a majalisar wakilai ta ƙasa da kuma ƙarin guda ɗaya da aka raɗa wa sunan, "kwamitin abinci da samar da abinci."
Daily Trust ta tattaro cewa Abbas ya sanar da sabbin shugabannin kwamitocin da mataimakansu a zaman mambobin majalisar na ranar Jumu'a, 1 ga watan Disamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ya bayyana sauye-sauyen da aka samu a kwamitocin jim kaɗan bayan kasafin kuɗin 2024 ya tsallaka zuwa karatu na biyu a zauren majalisar.
Honorabul Abbas ya karanto sunayen kana ya roƙi shugabanni da mataimaka masu barin gado su hanzarta miƙa ragamar kwamitocin ga sabbin da aka naɗa.
Wannan sauye-sauye na zuwa ne yayin da majalisar wakilan ke shirin fara sauraron ma'aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda zasu zo kare kasafinsu.
Da yake jawabi, Abbas ya ce:
"Wannan shi ne jerin sunayen ciyamomin kwamitoci da mataimakansu bayan an gyara su. Akwai buƙatar masu barin gado su mika ragama ga sabbin waɗanda suka maye gurbinsu cikin hanzari."
"Hakan na da matuƙar muhimmanci domin tattabar da zaman da za a fara da ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya ya tafi yadda ya dace."
Meyasa aka samu canji a kwamitocin?
Sake gyaran kwamitocin ya biyo bayan tsige wasu daga cikin ‘yan majalisar da kotun daukaka kara ta yi, Channels tv ta rahoto.
Kusan mambobin majalisar wakilai 15 ne suka rasa kujerunsu wanda hakan ya taba kwamitoci shiyasa aka yi gyara.
APC Ta Bukaci Kowa Ya Bi Yarjejeniyar Zaman Lafiya
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta zargi wasu shugabannin NNPP da saɓawa yarjejeniyar zaman lafiyam da suka sa wa hannu a hedkwatar yan sanda.
Mataimakin shugaban APC na Kano, Shehu Maigari, ya ce ya kamata 'yan sanda su ɗauki mataki domin a gabansu kowa ya sa hannu.
Asali: Legit.ng