Karancin Naira Ya Kara Tsanani, Bankuna Sun Ɗauki Mataki Kan Masu Zuwa Cire Kuɗi
- Matsalar karancin takardun Naira ta ƙara kunno kai duk da umarnin CBN na ci gaba da amfani da tsoho da sabon naira
- A jihar Ondo, bankuna sun kayyade adadin kudin da kowane kwastoma zai samu a rana saboda rashin wadatattun tsabar kuɗi
- Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake tunkarar bukukuwan kirsimeti na wannan shekarar 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Yayin da ake tunkarar bukukuwan kirsimeti nan da makonni uku, mutane sun fara cika bankuna suna neman tsabar kuɗi domin biyan buƙatunsu.
Amma rashin wadatattun tsabar kuɗin a ƙasa ya tilastawa bankuna rage adadin kuɗin da kwastomomi zasu iya cirewa a kowace rana a jihar Ondo.
A binciken da jaridar Leadership ta gudanar ta gano cewa mafi yawan mutane ba su samun damar cire adadin kuɗin da suke buƙata a kan kanta cikin bankuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankuna sun ɗauki mataki sabida rashin tsabar kuɗi
A wasu bankuna a Akure, babban birnin jihar Ondo, wasu kwastomomi sun shaida wa jaridar cewa ma'aikatan bankuna sun rage adadin kuɗin da kowa zai iya cirewa.
A cewar kwastomomin, ma'aikatan bankuna sun musu bayanin su yi amfani da wasu hanyoyin mu'amala da kuɗi a banki yayin biyan buƙatunsu.
Haka nan kuma an tattaro cewa da yawan bankuna a jihar Ondo sun fito aiki ne kawai amma babu isassun tsabar kuɗin da za su iya biyan buƙatun mutane.
A wasu bankuna a Akure, mutane na samun damar cire kuɗi daga asusunsu wanda bai wuce adadin N5,000 ba zuwa mafi yawa N20,000, daga nan ba ƙari.
Haka nan kuma akwai dogon layi a na'urorin cire kuɗi watau ATM da ke bankuna a babban birnin jihar.
Wannan lamari dai ya shafi masu sana'ar POS waɗanda a yanzu ba su samun wadatattun tsabar kuɗi daga bankuna ko ATM domin tafiyar da harkokin kasuwancinsu.
Karancin tsabar kuɗi ya ƙara tsananta
Wasu kwastomomin bankuna sun bayyana cewa wannan matsalar ta karancin tsabar kuɗi ta fara ne tun makon jiya.
Wata mata mai suna Misis Toyin Alade ta ce:
"Na zo Access da First Bank domin na cire N200,000 amma abu ya gagara, ma'aikatan bankin Access sun faɗa mun N100,000 zasu iya bani, haka na First Bank suka faɗa mun."
"Bankunan sun gaya mun babu tsabar kuɗi a ƙasa, maimakon haka sun bani shawarar na yi amfani da wasu hanyoyin wajen biyan buƙatuna."
Yadda aka sasanta rigimar siyasar jihar Ondo
A wani rahoton kwamishinar yaɗa labarai ta jihar Ondo ta bayyana yadda shugaba Tinubu ya sasanta rigimar siyasar gwamna da mataimakinsa.
Ta ce daga cikin matakan da shugaban kasar ya ɗauka, ya nemi mataimakin gwmana ya sa hannu a takardar murabus wadda ba kwanan wata.
Asali: Legit.ng