Edo: Dan Dako da Baro Ya Kashe Mai Karbar Haraji Kan Dalili Daya Tak

Edo: Dan Dako da Baro Ya Kashe Mai Karbar Haraji Kan Dalili Daya Tak

  • Mazauna birnin Edo sun shiga tashin hankali bayan da wani mai dan dako da baro ya kashe wani mai karbar haraji
  • An ruwaito cewa rigima ta hada su, lokacin da mai karbar harajin ya nemi dan dakon ya biya naira hamsin kudin tikiti
  • Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce dan dakon ya kashe mai karbar harajin daga bisani kuma ya kashe kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Edo - Wani dan dako da baro ya kashe wani mai karbar haraji a Benin City, jihar Edo kafin daga bisani ya kashe kanshi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma'a a kan titin Mission da ke karamar hukumar Oredo a jihar.

Kara karanta wannan

Dan shekara 18 ya fadi yadda ya kashe tsohuwar shugabar makaranta bayan sace wayarta a Ondo

Rundunar 'yan sanda/Jihar Edo
Wani dan dako ya kashe mai karbar haraji bayan cacar baki kan naira hamsin. Hoto: Nigerian Police
Asali: Facebook

Lamarin ya haifar da tashin hankali da tsoro a tsakanin mazauna yankin, inda masu shaguna suka rufe shagunansu tare da barin wajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kan naira hamsin dan dako ya kashe mai karbar haraji

An rawaito cewa an samu cacar baki tsakanin dan dakon da mai karbar haraji inda dan dakon ya ki biyan kudin tikiti na naira hamsin.

Jin haushin wannan cacar baki, aka rawaito mai karbar harajin ya hambarar da baron mutumin, inda kayan ciki suka watse, Daily Trust ta ruwaito.

Martani kan hakan, mai dakon ya zaro wuka tare da sokawa mai karbar harajin, wanda ya mutu nan take, ganin haka shi ma dan dakon ya kashe kanshi.

Gaskiyar abin da ya faru

Wani mazaunin wajen wanda ya ce a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mutane sun dade ana samun cin fuska daga masu karbar haraji a birnin Benin.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke mummunan hukunci kan Sarkin Fulani da wasu mutum 2 kan zargin garkuwa da mutane

"Ya yi kuskure yadda ya tunkari mai dan dakon. Amma bai kamata shi kuma ya kashe shi ba. Ana cikin mawuyacin hali, babu wanda ya san dan dakon na dauke da wuka.
"Mutane sun so su hana shi aikata kisan amma ya ki ji, daga bisani shi ma ya kashe daba wa kansa wukar, nan take ya mutu."

A cewar mutumin.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Chidi Nwanbuzo, ya tabbatar da faruwar lamarin, Legit ta ruwaito.

Gwamnati ta sallami fursunoni 332 a jihar Gombe da Kano

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta sanar da sallamar fursunoni 332 daga jihohi biyu na Arewacin Najeriya don rage cunkoso a gidajen gyara hali na kasar.

Daga jihar Kano ministan cikin gida ya sallami fursuononi 150, yayin da babbar jojin jihar Gombe ta sallami fursunoni 182 daga jihar Gombe, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.