An Fatattako Malamar Jinya Yar Najeriya Daga Ingila Saboda Yi Wa Mara Lafiya Addu’a
- Wata 'yar Najeriya da aikin jinya a wani asibiti a kasar Ingila ta taki rashin sa a yayin da hukumar asibitin suka sallameta daga aiki
- An rahoto cewa an kori malamar jinyar ne bayan da wani mara lafiya da take kula da shi ya kai kararta kan yi masa addu'a
- Ma'aikatan jinya su yi wa mara lafiya addu'a laifi ne babba a kasar Ingila, wanda ya ja 'yar Najeriya ta rasa aikinta tare da koroto gida
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An sallami wata malamar jinya 'yar Najeriya da ke aiki a kasar Ingila tare da maido da ita gida bayan samunta da laifin yi wa mara lafiya addu'a.
A wata wallafa da sanannen likitan Najeriya ya yi a shafinsa na 'X' @drolufunmilayo, ya bayyana cewa sabawa ka'idar aiki ne a Ingila a ga ma'aikacin jinya yana saka addini a aikinsa.
Ya ce duk da ba dai dai ba ne ma'aikacin jinya ya yi wa mara lafiya addu'a, sai dai su sanya malamin addini ya yi hakan, ko da kuwa mara lafiyar ne ya umurce su da yin hakan.
Olufunmilayo ya ce ya kawo wannan labarin ne domin ya gargadi likitoci 'yan Najeriya da ke shirin zuwa Ingila neman aiki, da su guji yi wa mara lafiya addu'a, Daily Trust ta ruwaito.
Likitan ya kara da cewa:
"Yi wa mara lafiyarka addu'a ana kallonsa kamar nuna gazawa ga aikinka da kuma saba ka'idar aikin. Kai naka kawai ka duba mara lafiya, sannan ka tsaya matsayinka"
Ga abinda ya rubuta a kasa:
Yar Najeriya ta rasa aikinta a Ingila bayan yi wa mara lafiya addu'a
Idan ba a manta ba Legit ta ruwaito maku cewa wata 'yar Najeriya da ke aikin jinya a kasar Ingila ta rasa aikinta sakamakon yi wa mara lafiya addu'a.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar gudanarwar asibitin sun gayyacin malamar jinyar don yi mata tambayoyi bayan da ta aikata abin da suke alakantawa da 'laifi'.
Malamar jinyar dai ta kasance mai kula da wata dattijuwa mai cutar ajali, inda ta durkusa tare da yi masa addu'a don samun saukin halin da take ciki.
Maras lafiyar ce aka ruwaito ta kai karar malamar jinyar, wacce bayan yi mata tambayoyi aka sallame ta daga aiki.
Uganda: Dattijuwa 'yar shekaru 70 ta haifi tagwaye
Asibitin karbar haihuwa da kula da mata na kasa-da-kasa da ke Uganda ya sanar da cewa dattijuwa 'yar shekaru 70 ta haihu a asibitin, Legit Hausa ta ruwaito.
A cewar asibitin a shafinsa na Facebook sun yi amfani da fasahar IVF akan dattijuwar, kuma tana cikin koshin lafiya bayan haihuwar.
Asali: Legit.ng