Jami’an Kwastam Sun Gano Muggan Makamai a Cikin Buhunan Shinkafa, Hotuna Sun Bayyana
- Jami'an hukumar kwastam sun yi babban kamu cike da nasara a karamar hukumar Imeko Afon ta jihar Ogun
- An kama wasu harsasai da aka nade a cikin buhunan shinkafa guda biyar a wani jeji da ke titin Palace/Ayetoro
- Nasarar ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu bayan shafe kimanin mako guda tana bibiyar masu fasa kaurin makaman
Jihar Ogun - Jami'an hukumar kwastam reshen Ogun, sun kama harsasai da aka nade a cikin buhunan shinkafa biyar sannan aka boye su a wani jeji a hanyar Palace/Ayetoro da ke karamar hukumar Imeko Afon ta jihar.
An cafke kayan ne a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, bayan samun wasu bayanan sirri wanda ya kai ga tura wasu jami'ai yankin domin tinkarar wadanda ke shigo da makaman cikin kasar.

Asali: Twitter
Yadda hukumar kwastam ta kama makamai a buhunan shinkafa
Mukaddashin kwanturolan kwastam na yankin Ogun Area 1, Mataimakin Kwanturola Amadu Shuaibu, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a iyakar Idiroko a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shuaibu ya ce kimanin mako guda kenan hukumar na bibiyar masu shigo da makaman har sai ranar Litinin da misalin karfe 5:00 na asuba lokacin da suka samu bayan sirri na makaman da aka nade a buhunan shinkafa biyar sannan aka boye su a jejin.
Ya ce:
"A yayin binciken, an gano harsasai kimanin guda 975 da aka boye a cikin buhunan."
“Mun kara zage damtse don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Shu’aibu ya ce illar fasa-kwaurin makamai da alburusai da ba a kula da su ba yana da muni, kama daga karfafa kungiyoyin masu aikata laifuka zuwa ga barkewar rikici da kuma yin kutse a harkokin tsaron kasa.

Kara karanta wannan
Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu ya ɗara caccakar Gwamnan PDP kan zaben jihar na 2024
An tilastawa barayi kwankwadar barasa
A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, ya nuno lokacin da aka tilastawa wasu barayi shan barasa da suka sata a wani babban kanti da ke kasar Afrika ta Kudu.
Wani dan jarida a Afrika ta Kudu, Velani Ludidi ne ya wallafa bidiyon, inda ya bayyana cewa barayin sun fasa kantin sannan suka saci giya.
Asali: Legit.ng