An Tilastawa Barayi Kwankwadar Giya da Suka Sata a Wani Babban Kanti, Bidiyon Ya Yadu a Gari
- Wasu mutane da ake zaton barayi ne sun gamu da bacin rana yayin da suka je sata a wani babban kanti a kasar Afrika ta Kudu
- An rahoto cewa barayin sun saci kwalaben giya da dama a kantin kafin aka kama su a washegari
- Ko da suka shiga hannu, mai kantin ya tilasta masu shanye gaba daya kwalaben giyan ko kuma ya dauki doka a hannunsa
Afrika ta Kudu - Wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, ya nuno lokacin da aka tilastawa wasu barayi shan barasa da suka sata a wani babban kanti da ke kasar Afrika ta Kudu.
Wani dan jarida a Afrika ta Kudu, Velani Ludidi ne ya wallafa bidiyon, inda ya bayyana cewa barayin sun fasa kantin sannan suka saci giya.
Ya kara da cewar a lokacin da aka kama barayin washegarin ranar da abun ya faru, mai shagon ya tilasta masu kwankwadar barasan ko kuma ya dauki doka a hannunsa.
Ya rubuta a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Barayi sun fasa shagon sannan suka saci giya da farashinsa ya kai 14k. An kama su washegarin ranar dauke da giyan. Mai kayan ya ce dole su shanye dukka a lokaci guda ko su fuskanci hukunci. Barayin suna ta fama."
A bidiyon, an gano wadanda ake zargin suna kwankwadar barasan daga kwalaben giyan.
Jama'a sun yi martani kan bidiyon barayi da aka tilastawa shan barasa
@Buchule_Putini:
"idan suka mutu, ba za a tuhumi mai shagon kan kisan kai ba?"
@Brahm_ZA:
"Amma wannan zai iya haddasa mutuwa. Gubar barasa ba wasa bane."
@LudidiVelani:
"Haibo, za su mutu ♂️"
@Ihhashi_Turkei:
"Wannan ne hukunci mafi kyau da na gani a shekarar nan "
Wani mutum ya ja kunnen yan coci
A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan gajeren bidiyo ya nuno lokacin da wani fusataccen mutum ya farmaki coci don nuna rashin jin dadinsa da yawan hayaniyarsu.
A cikin bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, mutumin ya shiga harabar kotun tare da karnukansa guda uku yayin da ake tsaka da bauta.
Da alama zuwansa cocin ya kawo karan tsaye ga taron addu'o'i da suke yi inda masu bauta suka fuskance shi, yayin da wasu suke kallo cike da kosawa.
Asali: Legit.ng