Allah Ya Yi Wa Shugaban NUGA Rasuwa Bayan Gajeruwar Rashin Lafiya

Allah Ya Yi Wa Shugaban NUGA Rasuwa Bayan Gajeruwar Rashin Lafiya

Mista Emeka Ogbu, Shugaban Kungiyan Shirya Wasannin Jami'o'i na Najeriya (NUGA), ya riga mu gidan gaskiya.

Farfesa Mohammed Bawa, mukadashin shugaban kungiyar, ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Laraba a Jos, babban birnin jihar Filato.

Shugaban NUGA ya riga mu gidan gaskiya
Shugaban NUGA, Emeka Ogbu, ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

Bawa ya ce Ogbu ya mutu a ranar Litinin bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta rahoto cewa a baya Ogbu shine daraktan sashin wasanni a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu (ESUT).

An zabe shi a matsayin shugaban NUGA a watan Maris na shekarar 2022.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164