Yanzun nan: An Rasa Rayuka da Yawa Yayin da Yan bindiga Suka Yi Artabu da Jami'an Tsaro
- Rayuka sun salwanta yayin da jami'an tsaro da yan bindiga suka yi artabu a jihar Anambra ranar Talata da safiya
- Rahoto ya nuna cewa musayar wutar ta ɗauki lokaci har sai da jami'an tsaron haɗin guiwa suka isa wurin, suka fatattaki yan ta'addan
- Kakakin yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai faɗi adadin mutanen da suka mutu ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Aƙalla rayuka huɗu suka salwanta yayin wata kazamar musayar wuta da ta auku tsakanin 'yan bindiga da jami'an tsaro a jihar Anambra.
Miyagun yan bindigan sun yi artabu da jami'an tsaron ciki harda yan sanda a ƙauyen Aguluzigbo, ƙaramar hukumar Anaocha ta jihar da ke Kudu maso Gabas.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa musayar wutar da aka yi da safiyar yau Talata, ta kwashe tsawon lokaci har sai da ƙarin jami'an tsaron haɗin guiwa suka kai ɗauki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun rasa rayukansu
Duk da ba a ƙayyade alkaluman yawan rayukan da aka rasa ba a musayar wutan, wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna aƙalla jami'an tsaro huɗu suka mutu.
Faifan bidiyon ya kuma nuna gawarwakin jami'an tsaron da ƴan ta'adda suka kashe a musayar wutan, ciki harda wani mutum ɗaya da ke kwance rai hannun Allah saboda raunukan da ya ji.
Yan sanda sun tabbatar da lamarin
Yayin da aka tuntube shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya bayyama cewa har kawo yanzu bai gama tantance alƙaluman waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon musayar wutan ba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Kakakin yan sandan ya yi alƙawarin cewa zai fitar da cikakken bayani a hukumance kan ainihin abin da ya auku nan ba da daɗewa ba.
A kalamansa ya ce:
"Na samu labarin abinda ya auku amma ban tabbatar da adadin waɗanda suka rasa rayukansu. Dakarun yan sanda sun dakile harin kuma suna wurin domin dawo zaman lafiya a yankin."
Yan Sanda Sun Halaka Hatsabiban Yan Bindiga Uku
A wani rahoton na daban Yan sanda da haɗin guiwar dakarun rundunar yan sa'kai sun halaka kasurguman yan bindiga uku a jihar Katsina.
Kwamishinan yan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa, ya ce an kashe yan ta'addan ne yayin sintirin jami'an tsaro a Jibia.
Asali: Legit.ng