'Yan Bindiga Sun Bude Wa Dakarun 'Yan Sanda Wuta, Sun Halaka Rayuka da Yawa a Jihar APC
- Yan bindiga sun farmaki jami'an 'yan sanda a shingen bincike, sun halaka biyu daga cikinsu a jihar Imo
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da haka ranar Litinin, ta ce maharan sun kashe farar hula mutum ɗaya da ya zo wucewa
- Jihar Imo da sauran jihohin Kudu maso Gabas sun jima suna fama da hare-haren yan bindiga kan jami'an tsaro da wuraren ibada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Miyagun yan bindiga sun halaka ƴan sanda biyu da wani mutum ɗaya yayin da suka kai hari shingen binciken ababen hawa a jihar Imo.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Imo ce ta bayyana haka ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Yan bindigan sun aikata wannan mummunan ɗanyen aikin ne a mahaɗar titunan Ahiara a ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise, jihar Imo, lamarin da ya jefa mutane cikin fargaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan na isa shingen binciken, suka buɗe wa jami'an 'yan sandan wuta, nan take biyu daga ciki suka rasa rayukansu.
A cewar majiyoyin, yan bindigan sun kashe farar hula mutum ɗaya, wanda ya zo wucewa ta wurin, harsashin bindiga ya yi ajalinsa, Leadership ta ruwaito.
Wane mataki hukumar ƴan sanda ta ɗauka?
A sanarwan da kakakin hukumar yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya fitar ranar Litinin, ya ce tuni aka tashi rundunar jami'an tsaron haɗin guiwa suka bazama da nufin kamo maharan.
Ya ce kwamishinan ƴan sanda, CP Ɗanjuma Aboki, kwamandan sojojin birged ta 34 da jami'an sa'kai JTF, sun kewaye wurin da lamarin ya faru domin cafke ƴan bindigan.
Har yanzu dai babu ƙungiyar da ta fito ta ɗauki nauyin wannan harin, amma shiyyar Kudu maso Gabas ta jima tana fama hare-hare kan jami'an tsaro, coci-coci da sauransu.
A yan shekarun da suka shuɗe, yan sanda da sauran jami'an hukumomin tsaro da dama sun rasa rayukansu a irin waɗannan hare-hare na ta'addanci.
An Gano Gawar Shugaban Fulanin da Ya Ɓata
A wani rahoton na daban A karshe dai an gano gawar shugaban Fulani, Umar Ibrahim, wanda ya ɓata a yankin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.
Shugaban wata ƙungiyar Fulani ya ce an tsinci gawar ne a cikin wata tsohuwar rijiya tare da sojojin Operation Safe Haven.
Asali: Legit.ng