Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Yi Wani Muhimmin Abu 1 Kan Gidan Shehu Shagari da Gobara Ta Kona

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Yi Wani Muhimmin Abu 1 Kan Gidan Shehu Shagari da Gobara Ta Kona

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta bayar da umarnin gyara gidan tsohon shugaban ƙasa Shehu Shagari wanda gobara ta ƙona a makon jiya
  • Gwamnan jihar Ahmed Aliyu wanda ya bayar da umarnin lokacin wata ziyara gani da ido da ya kai gidan ya faɗi muhimmancin da gidan ya ke da shi
  • Gwamnan ya jajantawa iyalan tsohon shugaban ƙasar tare da addu'ar Allah ya kiyaye aukuwar irin wannan bala'in a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu Sokoto, ya bayar da umarnin sake gyara gidan tsohon shugaban ƙasa Shehu Shagari gaba ɗaya wanda gobara ta ƙone a makon jiya.

Gwamnan ya bada umarnin ne a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba jim kaɗan bayan ya ziyarci gidan domin tantance irin ɓarnar da gobarar ta yi, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Gwamnatin Sokoto za ta gyara gidan Shehu Shagari
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayar da umarnin gyara gidan Shehu Shagari Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Ya bayyana gobarar a matsayin bala'i kuma abin takaici, inda ya bayyana gidan da ya ƙone a matsayin mai tarihi ba wai ga jihar Sokoto kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"A gare mu, wannan gidan yana da matuƙar muhimmanci a tarihi kasancewar gidan tsohon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na farko a Najeriya Shehu Usman Aliyu Shagari."
"Kamar abin tarihi ne ga masu tasowa, saboda haka za mu gyara wannan gidan."

Yayin da yake jajantawa iyalan marigayi shugaban ƙasar kan gobarar, Aliyu ya roƙi Allah maɗaukakin Sarki da ya kiyaye sake aukuwar lamarin.

Wasu daga cikin iyalan tsohon shugaban ƙasar ne suka zagaya da gwamnan ɓangaren da gidan ya ƙone.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Sokoto, mai suna Malam Dalhat wanda ya yaba da wannan matakin da gwamnan ya ɗauka na gyara gidan.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugaban APC a jihar arewa

Malam Dalhat ya bayyana cewa abu ne mai kyau gwamnan ya yi duba da yadda gidan yake da mutunci da martaba a idanun ƴan jihar Sokoto da ma Najeriya baki ɗaya.

"Wannan gyaran ya dace sosai domin martaba gidan ne saboda yana da ɗumbin tarihi a ƙasa." A cewarsa.

Gwamna Aliyu Ya Umarci Wasu Ma'aikata Su Yi Murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya umarci ma'aikatan da aka naɗa a matsayin sakatarorin ƙananan hukumomi da su yi murabus.

Gwamnan na jam'iyyar APC ya umarci su gaggauta yin murabus ne saboda muƙaman da aka naɗa su na siyasa ne

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng