“Duk Namijin da Ya Aureni Ya Taki Sa’a”: Budurwa Mai Hannu Daya Ta Yaba Surar Da Allah Ya Yi Mata
- An gano wata matashiyar budurwa wacce ke da hannu daya tana rawa tare da baje koli surar jikinta a bidiyon TikTok da ya yadu
- Matashiyar ta ce komai ya ji a jikinta sannan ta bugi kirjin cewa duk mutumin da ya aureta ya taki sa'a
- Bidiyon ya yi fice a TikTok yayin da mutane da dama suka amince da ikirarin budurwar sannan suka jinjina kyawunta a sashin sharhi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata kyakkyawar budurwa wacce ke da hannu daya ta yada wani bidiyo a TikTok inda ta ce komai ya ji a jikinta.
A cikin bidiyon, matashiyar mai suna Maryann Officiall, ta zage tana kwasar rawa a cikin wani daki tana mai baje kolin dirarren surar jikinta mai matukar kyau.
Ta bayyana karara cewa duk mutumin da ya aureta yana da matukar sa'a a rayuwa saboda mutumin ya samu kyakkyawar mace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da kasancewarta mai bukata ta musamman, Maryann na iya bakin kokarinta don ganin ta kasance cikin farin ciki a rayuwa.
Shafinta na TikTok na kunshe da tarin bidiyoyi da ke nuno ta tana rawa da baje kolin kyawunta.
Ta yi wa sabon bidiyon take da:
"Mijina na da sa'a ba kadan ba, kalli cikakken kaya mana. Kana zolayata ne."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani kan bidiyon kyakkyawar mata mai hannu daya
@Janice B ta ce:
"Shin wai har mutane sun manta halin da matar nan ta shiga ne? Ko dai sabbin zuwa ne ke yin martani mara dadi? Ina zuciyarku na tausayi?"
@Shamaunbeatable ta ce:
"Wasu mutane basu da hankali da tausayi. Dubi irin martanin da suke ajiyewa. Allah ya kyauta."
@user6168777203075 ya ce:
"Ci gaba da gashi. Wasu da suke da hannu basu cimma abun da kika cimma ba. Don Allah kada ki kula wadannan martanin marasa dadi."
@mofieyisetanire ta ce:
"Ba a yi wa wasu horo da soyayya ba, ina mamakin wasu mutane za su iya rubuta irin wannan martanin."
Makudan kudaden da dan agaji ke samu
A wani labarin, mun ji cewa wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya yana samun albashi N204k duk kwanan duniya a matsayin ma'aikacin agaji.
Mutumin ya wallafa wani bidiyo a TikTok don bayar da labarinsa amma ya ce aikin sam babu sauki saboda yana kula da wani tsoho ne.
Asali: Legit.ng