Yan Sanda Sun Bayyana Kwakkwaran Dalilin Hana Zanga-Zanga a Kano

Yan Sanda Sun Bayyana Kwakkwaran Dalilin Hana Zanga-Zanga a Kano

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓen gwamna Abba Yusuf na Kano bisa hujjar cewa shi ba sahihin ɗan jam'iyyar sa ta NNPP ba ne
  • Sai dai, takardun hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke, sun nuna cewa Yusuf ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a 2023
  • Hakan ya ƙara dagula al'amura a jihar Kano, kuma ya kai ga magoya bayan APC da NNPP shirya zanga-zanga, sai dai ƴan sandan sun ce ba za su bari a yi zanga-zanga ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kano, jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gargadi ƴan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar kan zanga-zangar da suka shirya yi.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun tura gargadi ga jam'iyyun APC, NNPP kan shirin zanga-zanga a jihar

Manyan jam'iyyun biyu na Kano sun shirya gudanar da zanga-zanga a lokaci guda a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamban 2023.

Yan sanda sun hana zanga-zanga a Kano
Yan sanda sun haramta zanga-zanga a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasiru Gawuna
Asali: Facebook

Ƴan sanda sun haramta zanga-zangar da NNPP, APC suka shirya

Hakan dai ya biyo bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke a baya-bayan nan, inda ta tabbatar da soke zaɓen Gwamna Abba da kotun zaɓe ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a martanin da rundunar ƴan sanda jihar ta yi kan zanga-zangar da aka shirya yi, ta ce ba ba ta bayar da damar yin hakan ba, kuma duk wanda ya karya umarninta zai fuskanci hukunci.

Sanarwar ta fito ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba, ta hannun mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, a madadin Kwamishinan ƴan sandan jihar, Husaini Gumel, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Abubuwa 2 na sani yayin da kotun daukaka kara ke yanke hukunci kan soke zaben gwamnan Nasarawa

Jaridar Channels tv ta rahoto cewa ƴan sandan sun fusata kan zanga-zangar da aka shirya, suna masu cewa hakan zai kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Waɗanda ke shirin shiga zanga-zangar an shawarci su sake tunani, su haɗa kai da jami'an tsaro, kuma su daina ayyukan da ka iya yin barazana ga zaman lafiya."

Amnesty International Ta Fusata Kan Cafke Masu Zanga-Zanga a Kano

A wani labarin kuma, ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty Internationl, ta yi magana kan cafke masu zanga-zanga a Kano.

Ƙungiyar ta yi tir da matakin da yan sanda suka ɗauka na cafke wadanda suka hau kan tituna domin zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng