Gwamnan APC Ya Ɗau Zafi, Ya Dakatar da Kwamishina da Wani Babban Hadimi Kan Abu 1 Tak
- Gwamnan jihar Imo ya dakatar da kwamishinan filaye, bincike da tsare-tsare, Honorabul Noble Atulegwu, daga muƙaminsa nan take
- Ya kuma dakatar da mai ba gwamna shawara kuma babban manajan hukumar gidaje ta jihar, Mbakwe Obi Jnr, ya umarci su bar ofis
- Sai dai Gwamnatin jihar Imo ba ta bayyana makasudin ɗaukar wannan mataki ba amma an ce ba zai rasa nasaba da wata taƙaddama kan filaye ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya dakatar da kwamishinan filaye, bincike da tsare-tsaren fili, Honorabul Noble Atulegwu, daga muƙaminsa.
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, dakatarwan da gwamnan na APC ya yi wa kwamishinan zata fara aiki ne nan take.
Sakataren gwamnatin jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Chief Cosmas Iwu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka, sakataren gwamnatin ya sanar da cewa Gwamna Uzodinma ya amince da dakatar da mai ba shi shawara ta musamman kuma manajan hukumar gidaje, Honorabul Mbakwe Obi Jnr.
A sanarwan da SSG ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, ya ce:
"Gwamnan jihar Imo, mai girma Sanata Hope Uzodinma, ya amince da ɗaukar matakin dakatarwa nan take kan kwamishinan filaye, bincike da tsare-tsare, Honorabul Noble Atulegwu."
"Mai girma gwamnan ya kuma amince da dakatar da mai bada shawara na musamman kuma shugaban hukumar gidaje ta jihar Imo, Honorabul Mbakwe Obi Jnr nan take daga ofis."
Meyasa Gwamna Uzodinma ya ɗauki wannan mataki?
Sanarwan ba ta bayyana dalilin da ya sa Gwamna Uzodinma ya zaɓi ɗaukar matakin dakatarwa daga Ofis kan manyan hadiman nasa guda biyu ba.
Amma jaridar ta attatro cewa kwamishinan da aka dakatar, Atulegwu, na rigima da wasu yankuna kan mallakar filaye a jihar, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A ƙarshe, gwamnatin Imo ta umarci kwamishinan da SA su miƙa ragamar jagoranci ga babban jami'i da ke ƙasa da su a ma'aikatun, su tattara su bar ofis.
Taron NEC ya kankama a Villa
A wani rahoton na daban Sanata Kashim Shettima da gwamnonin jihohin Najeriya na PDP, APC da LP sun shiga taron NEC yanzu haka a fadar shugaban kasa.
Mataimakin shugaban ƙasar na jagorantar taron NEC karo na huɗu tun bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng