Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Gwamnonin APC da PDP a Villa, Bayanai Sun Fito

Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Gwamnonin APC da PDP a Villa, Bayanai Sun Fito

  • Sanata Kashim Shettima da gwamnonin jihohin Najeriya na PDP, APC da LP sun shiga taron NEC yanzu haka a fadar shugaban kasa
  • Mataimakin shugaban ƙasar na jagorantar taron NEC karo na huɗu tun bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamnonin jihohi 36, ministan Abuja da ministan kuɗi, gwamnan CBN da shugaban NNPCL na cikin mambobin NEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, na jagorantar taron majalisar tattalin arziki ta ƙasa (NEC) karo na 137 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Taron majalisar tattalin arzikin kasa NEC.
Kashim Shettima Na Jagorantar Taron NEC a Fadar Shugaban Kasa a Abuja Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Mambobin majalisar ƙolin tattalin arzikin ƙasa (NEC) sun haɗa da baki ɗaya gwamnonin jihohi 36 da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta amince da wani muhimmin nadin da Shugaba Tinubu ya yi

Sauran waɗanda ke cikin wannan majalisa sune ministan kuɗi, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL) da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan taro na NEC da ke gudana yanzu haka a Villa shi ne na huɗu a gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jerin waɗanda suka halarci zaman NEC a Villa

Waɗanda aka hangi sun hakince a kujerun da aka tanadar musu a ɗakin taron NEC sun kunshi dukkan gwamnonin jihohin Najeriya ban da na jihohi tara.

Jihohin takwas daga cikin jihohin da gwamnoninsu ba su halarci zaman ba, Akwa Ibom, Kano, Legas, Enugu, Osun, Borno, Nasarawa da Adamawa sun tura mataimakansu su wakilce su.

Amma ba a ga Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ko mataimakinsa, Philip Shaibu, ba domin kujerar da aka ware musamman domin jihar Edo babu kowa har yanzu.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamna, shugaban majalisar dokoki da mataimakinsa sun yi murabus a jihar arewa

Ana tsammanin taron NEC na yau Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023 zai ɗauki dogon lokaci, amma ba a faɗi muhimman batutun da za su maida hankali ba, rahoton The Nation.

'Lafiyar Tinubu kalau in banda tiyatar da aka masa tun 2021'

A wani rahoton na daban Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa lafiyar Shugaba Tinubu kalau ba abinda ke damunsa in banda kafar da aka masa tiyata

Mai ba shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce tun tiyatar da aka yi wa Tinubu a guiwa a 2021 har yau yana jinya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262