Gwamnatin Tinubu Ta Sake Tsokano Fada da Kungiyoyin Kwadago

Gwamnatin Tinubu Ta Sake Tsokano Fada da Kungiyoyin Kwadago

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rage kuɗin da aka ware na ƙarin albashi ga ma'aikata a ƙarin kasafin kuɗi da Naira biliyan 100
  • Kungiyoyin ƙwadagon sun yi fatali da matakin, inda suka bayyana hakan ya saɓa yarjejeniyar da suka yi da gwamnati
  • Ƙungiyar ƙwadagon ta ce hakan zai zama daidai ne idan gwamnati ta rage kuɗaɗen da take kashewa ta hanyar rage hadimai masu yawa da ta ɗauka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun yi fatali da matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na rage kuɗin ƙarin albashi ga ma'aikatan gwamnatin tarayya a ƙarin kasafin kuɗi da Naira biliyan 100.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun yi gargadin cewa wannan ba yarjejeniyar da suka yi da gwamnati ba ce kuma za su bijire wa hakan, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Kano: Kotun daukaka kara ta bukaci lauyoyi su dawo da takardun hukuncin da ta yanke

Kungiyoyin kwadago sun caccaki FG
Kungiyoyin kwadago sun caccaki gwamnatin tarayya Hoto: @NLCHeadquarters/@officialABAT
Asali: Twitter

Tun da farko dai gwamnatin tarayyar ta ware N210bn a cikin ƙarin kasafin kuɗin domin yin ƙarin albashi ga ma'aikata na tsawon wata uku, sai dai a ƙarin kasafin kuɗin da aka amince da shi, an zaftare kuɗaden sun dawo N110bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin ƙwadago sun caccaki matakin

Mataimakin babban sakataren ƙungiyar ta NLC, Chris Onyeka, ya ce hakan zai yi daidai ne idan gwamnati ta yanke shawarar rage yawan hadimai da mataimakan da ta ɗauka.

Darektan yaɗa labaran NLC, Benson Upah, ya bayyana cewa:

“Ba a sanar da mu ba kafin a yi haka. Duk da haka, wannan dabi'ar ba sabun abu bane ga irin tunanin wannan gwamnatin. Abun akwai baƙin ciki."

Mataimakin shugaban TUC na ƙasa, Tommy Etim, ya gargadi gwamnatin tarayya game da wasa da ƙarin albashin ga ma'aikatan Najeriya.

"Yarjejeniya ce da aka cimmawa da ƙungiyoyin kwadago kuma an ajiye takardun yarjejeniyar da da aka cimma a kotu." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai farmaki a gona, sun yi awon gaba da matan aure 8

NLC, TUC Sun Ba FG Sharaɗi

A wani labarin kuma, ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun gindaya wa gwamnatin tarayya sharuɗɗansu kafin su janye yajin aikin da su ke yi.

Ƙungiyoyin dai sun lissafo sharuɗɗa shida da su ke so gwamnatin tarayyar ta cika kafin su amince su janye yajin aikin da su ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng