Yadda Mai Tallar Gyada Ta Zama Miloniya, Bidiyon Sauyawarta Ya Girgiza Intanet

Yadda Mai Tallar Gyada Ta Zama Miloniya, Bidiyon Sauyawarta Ya Girgiza Intanet

  • Wani labari mai ban sha'awa ya bayyana yayin da wata budurwa ta nunawa duniya sauyawar da tayi bayan yan shekaru
  • Jajirtacciyar matashiyar ta yada bidiyon sauyawarta daga mai tallar gyada zuwa attajira mai ban mamaki
  • Sauyawarta ya cika masu amfani da soshiyal midiya da mamaki yayin da wasu da dama suka yi fatan samun irin yanata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani labari mai ban sha'awa na jajircewa da sauyawar wata matashiyar budurwa ya ja hankalin jama'a a soshiyal midiya.

Matashiyar mai suna @tiwasmith1 wacce ta fara a matsayin mai tallar gyada a titi, ta sauya gaba daya inda ta zama tamkar wata sarauniya, tana mai baje kolin kwaliyyarta a TikTok.

Kara karanta wannan

"Bana iya ajiye ko kwabo yanzu": Dan Najeriya da ke karbar N200k duk wata ya koka da tsadar rayuwa

Daga tallar gyara ta zama miloniya
Yadda Mai Tallar Gyada Ta Zama Miloniya, Hotunan Sauyawarta Ya Girgiza Intanet Hoto: @tiwasmith1/TikTok.
Asali: TikTok

Tsohuwar mai tallar gyada ta ce yanzu ita miloniya ce

A cewar matashiyar wacce ke cike da farin ciki, ta fara rayuwarta a matsayin yar talla amma duk da haka, ta zama mai nasara a rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daga mai tallar gyada zuwa miloniya. Nagode Allah da sauyin", ta rubuta.

Martanin jama'a kan sauyawar mai tallar gyada

Yayin da bidiyon matashiyar ya samu karbuwa a soshiyal midiya, jama'a sun yaba da inda ta kai a rayuwa.

Mutane da dama sun nuna sha'awarsu a kan jajircewarta da kuma sauyawar da ta yi.

@Benzucker musik ta ce:

"Don Allah ke kika lashe gasar jor."

@loner ta yi martani:

"Na tuna ki, na taba siyan gyada a wajenki wani lokaci haka ma shaa Allah lallai kin kara sheki."

@hunny bunny sometimes ta yi martani:

"Kada ka yanke hukunci da ganin yanayin mutum saboda wannan mutumin na iya sauya rayuwarka kuma koda dai ban san ki ba lallai kin yi."

Kara karanta wannan

Duk da mijina yana kakada min duka, bana son a raba auren mu, mata ta fadawa kotu a Kaduna

@PROMISE ta yi martani:

"Ba zan taba bude ki ba."

Bidiyon mace mai kamar maza da gemu

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiya ta yi fice a TikTok bayan ta saki wani dan gajeren bidiyo don nunawa mutane gemun da take dauke da shi a fuskarta.

Kyakkyawar matar, Sarah Anane, ta ja hankalin muane saboda fuskarta na dauke da gemu kamar na maza.

Sarah ta daura bidiyoyi da dama a shafinta tana mai nunawa duniya fuskarta ta musamman, wanda ke cike da gashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng