Har Yanzu Shugaba Tinubu Na Jinyar Tiyatar da Aka Masa a Gwiwa, in Ji Onanuga

Har Yanzu Shugaba Tinubu Na Jinyar Tiyatar da Aka Masa a Gwiwa, in Ji Onanuga

  • Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa lafiyar Shugaba Tinubu kalau ba abinda ke damunsa in banda kafar da aka masa tiyata
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce tun tiyatar da aka yi wa Tinubu a guiwa a 2021 har yau yana jinya
  • A cewarsa, bayan wannan babu abin da ke damun shugaban ƙasa kuma ba a ɓoye wa yan Najeriya komai ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa har yanzu Shugaba Bola Tinubu na jinyar tiyatar da aka masa a gwiwa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Har yanzu shugaba Tinubu na jinyar tiyatar da aka masa a guiwa, in ji Onanuga Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Idan zaku iya tunawa a shekarar 2021, kimanin shekaru biyu kenan da suka wuce, Bola Ahmed Tinubu ya je an masa tiyata a guiwarsa a birnin Landan na ƙasar Ingila.

Kara karanta wannan

"Laifin ka ne": Hadimin Tinubu ya fadi abu 1 da Obasanjo ya yi da ya sa kasar nan a mawuyacin hali

An yi masa wannan aiki a ƙafa ne gabannin harkokin yaƙin neman zaɓe ya kankama a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu na cikin ƙoshin lafiya - Onanuga

Da yake amsa tambayoyi kan yanayin lafiyar shugaban ƙasa a wata hira da jaridar Tribune, Onanuga ya ce babu wata cuta da ke damun Shugaban kasa amma har yanzu yana jinyar tiyatar gwiwa.

A kalamansa, hadimin shugaba Tinubu ya ce:

"A'a lafiyarsa kalau, mun faɗawa yan Najeriya, shugaba Tinubu na cikin ƙoshin lafiya a lokacin da ake tunkarar zabe. Tun kafin fara kamfe, ina ga shekara ɗaya kafin haka, ya je aka masa tiyata a guiwa."
"Ba a ɓoye batun wannan tiyata ba kowa ya sani domin har shugaban kasa a wancan lokacin, Muhammadu Buhari, ya je gaishe shi a Landan lokacin da yake murmure wa."
"Idan aka maka tiyatar guiwa ba zai yiwu ka riƙa tafiya kamar ɗan shekara 25 ba, na san har yau yana jinyar ƙafarsa saboda babbar tiyata ce. Ban da wannan ba abinda ke damunsa."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ne ya sa kotu ta tsige Abba Gida-Gida da gwamnonin PDP 2? Gaskiya ta fito daga Villa

Buhari Ya Faɗi Manufa 1 Tal da Ta Sa Ya Canza Takardun Naira

A wani rahoton na daban Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmin dalilin da ya sa gwamnatinsa ta canza fasalin Naira ana dab da zaɓen 2023.

Yan Najeriya sun sha baƙaɗ wahala loƙacin da aka yi wannan canjin kuɗin wanda gwamnan CBN na wancan lokacin, Godwin Emefiele, ya aiwatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262