Nasara: Dakarun Sojoji Sun Buɗe Wa Tawagar 'Yan bindiga Wuta, Sun Kashe Su da Yawa a Arewa
- Sojojin rundunar OPSH sun halaka yan bindiga bakwai a ƙaramar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna
- Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Oya James, ya ce sojojin sun kwato muggan makamai daga hannun yan ta'addan
- Ya ce a makon jiya kaɗai, sojojin sun kubutar da mutane 15 da aka yi garkuwa da su kuma sun dakile hare-haren yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Jami'an sojojin rundunar Operation Safe Haven (OPSH) sun samu nasarar murƙushe ƴan bindiga bakwai har lahira a ƙaramar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, bayan kashe ƴan ta'addan, sojojin sun kwato makamai masu yawa daga hannunsu.
Wannan nasara na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin OPSH, Kaftin Oya James, ya fitar ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yayin da sojojin suka fita sintiri cikin shirin yaƙi, kwatsam suka haɗu da ƴan bindigan a filin Kachallah, inda ba tare da bata lokaci suka buɗe musu wuta aka yi artabu mai tsanani.
A cewarsa, sakamakon musayar wutar ne sojojin suka tura ƴan bindiga shida zuwa lahira kana sauran suka tsere ɗauke da raunukan harsashin bindiga.
A rahoton Guardian, kakakin OPSH ya ce:
“Sojoji sun bincike yankin inda suka kwato bindiga kirar AK 47 guda daya, magazine 2, alburusai 52 mai nauyin 7.62mm, babur daya, wayoyin Tecno 2, fakiti 2 na taba sigari, da wasu alburusai iri-iri."
Dakarun sun kashe wani hatsabibin ɗan bindiga
Ya ƙara da cewa sojojin sun yi nasarar kashe wani da ake zargin dan fashi ne, Musa Wada a wani samame da suka kai a kauyen Kondo da ke karamar hukumar Zangon Kataf.
Ya kuma bayyana cewa an kama mutane 33 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin makon da ya gabata.
James ya ce:
“Bugu da kari, an kubutar da mutane 15 da aka yi garkuwa da su, an dakile hare-hare uku da aka kai kauyuka, sannan an kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa guda takwas."
Kannywood ta yi babban rashi
A wani rahoton na daban Allah ya yi wa shahararren darakta a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Aminu S Bono, rasuwa ranar Litinin.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya tabbatar da rasuwar daraktan a shafinsa na soshiyal midiya
Asali: Legit.ng