Majalisar Dattawa Ta Amince da Wani Muhimmin Nadin da Shugaba Tinubu Ya Yi
- Majalisar dattawa a ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio ta amince da naɗin Dakta Agbasi a matsayin MD na hukumar FERMA
- Amincewa da naɗin ya biyo bayan buƙatar hakan da Shugaba Tinubu ya yi a gaban majalisar dattawan
- Majalisar ta kuma amince da naɗin wasu mutum tara a matsayin mambobin gudanarwa na hukumar FERMA bayan an tantance su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT Abuja - A ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba majalisar dattawa ta amince da naɗin Dakta Chukwuemeke Agbasi, a matsayin Manajan Daraktan Hukumar Kula da Tituna Gwamnatin Tarayya (FERMA).
Haka kuma majalisar ta tabbatar da naɗin wasu mutum tara a matsayin mambobin gudanarwa na hukumar ta FERMA, cewar rahoton Nigerian Tribune.
Ku tuna cewa wasiƙar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rubuta a hukumance yana neman buƙatar majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen mutum 11 da ya naɗa, an karanta ta a zauren majalisar a ranar 1 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wanene sauran waɗanda aka amince da naɗinsu?
Jaridar TheCable ta ce wadanda aka tabbatar da naɗinsu tare da Dakta Agbasi sun haɗa da, Mista Terms Manasseh, Dakta Kenneth Ugbala, Sanata Timothy Aduda da Mista Babatunde Daramola.
Sauran sun haɗa da Mista Preye Oseke, Aminu Adamu Papa, Mista Abubakar Bappa, Shehu Mohammed da Yusuf Othmam.
Tabbatar da naɗin nasu ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattijawa kan FERMA da Sanata Hussaini Uba ya jagoranta wanda ya tantance waɗanda aka naɗa gabaɗayan su.
Da yake miƙa rahotonsa, Sanata Uba ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da bukatar Shugaba Tinubu na amincewa da waɗanda aka naɗa kamar yadda sashe na 2 (1) (2) na dokar FERMA ta shekarar 2002 ya tanada.
Shugaba Tinubu Ya Soke Nadin Shugaban FERMA
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soke naɗin matashin shugaban hukumar FERMA da ya yi.
Shugaban ƙasar ya soke naɗin Injiniya Imam Kashim Imam ne biyo bayan cece-kucen da naɗinsa ya haifar a faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng