“Gwamnonin Gobe Koda Basu Iya Ba”:Wasu Yara Sun Cika da Murnar Ganin Malaminsu Yana Zuba Turanci

“Gwamnonin Gobe Koda Basu Iya Ba”:Wasu Yara Sun Cika da Murnar Ganin Malaminsu Yana Zuba Turanci

  • Wani bidiyon TikTok da ke nuna yan samari suna mamakin yadda sabon malaminsu ke zuba Turanci ya yadu
  • Daliban, wadanda suka mamaye malamin nasu a kamara, suna ta hira da shi cike da farin ciki da annashuwa
  • Shima ya cika da mamakin ganin cewa yaran basu iya Turanci ba sosai, inda malamin ya ce shi ya iya Turanci, Yarbanci da Hausa sosai

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyo mai jan hankali a TikTok ya nuno yadda wasu matasan yara suka cika da mamaki kan yadda sabon malaminsu ke zuba Turanci cikin kwarewa.

Daliban wadanda suka taru a kusa da malamin da ke bayan kamara, sun yi ta hira da shi cikin sakewa.

Kara karanta wannan

“Yadda na koma kwana a karkashin gadar Oshodi bayan shafe shekaru 21 a Amurka,” wani mutum ya koka

Yan makaranta tare da malaminsu
“Gwamnonin Gobe Koda Basu Iya Ba”:Wasu Yara Sun Cika da Murnar Ganin Malaminsu Yana Zuba Turanci Hoto: TikTok/@emma.oniru
Asali: TikTok

Ya nuna mamakinsa ganin cewa basu jin Turanci sosai, wanda shine yaren hukuma a Najeriya. Cike da alfahari, malamin ya sanar da cewar ba Turanci kadai yake ji ba, harma da Yarbanci da Hausa, wadanda suna daga cikin manyan yaruka a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Lucia ta yi martani:

"Ku yi ta wasa wadannan yaran sune za su zama shugabannin kasarku a gobe yan arewa basu da ilimin boko amma mu muka fi kowa karbar shugabanci."

Jamesphilip907:

"Sanatoci da gwamnonin gobe."

Classynana:

"Duk da haka sun fi wasu daliban Yarbawa ku zo makarantar N.U.D gram a jihar Ogun za ku ji baaba ni bana jin turanci.”

Abba Sadiq:

"Ina alfahari da su, suna son su koya."

Kara karanta wannan

“Da na koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari ya magantu kan zaryar da wasu ke yi a gidansa na Daura

Abdullawal58:

"Shin hakan na nufin idan mutum bai iya Turanci ba shi jahili ne? A'a jahilci baya shafan yare."

James Joshua:

"Zan so na yi hidimar kasa a Arewa."

Dtdso:

"Hausa ne yarena kadai ya isa. Suna alfahari da fadin haka. Turanci yarenmu ne? Hausa ne ya kamata ya zama yaren kowa a Najeriya."

Yan Najeriya za su iya karatu kyauta

A wani labarin, mun ji cewa ofishin jakadancin Faransa, ya sanar da fara karbar takardun 'yan Najeriya masu sha'awar yin karatun digiri na biyu a fannoni daban-daban na ilimi a kasar.

Legit.ng ta fahimci cewa, ana karbar takardar shaidar kammala karatun HND a shirye-shiryen da mutum zai nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng