Ana Tsaka da Jimamin Korarsa a Gwamnan Kano, Abba Ya Tura ’Ya’yan Talakawa 150 Karatu a India

Ana Tsaka da Jimamin Korarsa a Gwamnan Kano, Abba Ya Tura ’Ya’yan Talakawa 150 Karatu a India

  • Akalla Kanawa 150 ne suka samu cikakken tallafin karatu don ci gaba da karatun digiri na biyu a waje
  • Tallafin da aka ba wadannan dalibai ya samu amincewar Gwamna Abba Yusuf bayan da kotun daukaka kara ta soke zabensa
  • An tattaro cewa an zabo wadannan dalibai ne daga cikin dalibai 1,001 ‘yan asalin jihar Kano da ke fadin kananan hukumomin jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Kano - Biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke zabensa, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da rukuni na hudu da ya kunshi dalibai 150 zuwa kasar India don yin digiri na biyu.

Daliban sun tafi India ne daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano kafin a bayyana hukuncin kotun, wanda ya tabbatar da hukuncin da kotun kararrakin zabe da ta ba Gawuna gaskiya.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun daukaka kara: Farfesan arewa ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a Kano

Abba Gida-Gida ya tura dalibai karatu India
Gwamnan Kano ya tura dalibai karatu India | Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Sai dai duk da wannan koma-baya, Gwamna Yusuf na NNPP ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwar zai yi nasara a kotun koli, rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zabo dalibai 150 daga 1,001 'yan asalin Kano, inji gwamnati

A cewar gwamnati, an zabo daliban 150 'yan asalin jihar Kano 1,001 domin daukar nauyinsu su yi digiri na biyu a kasashen waje, rahoton Tribune Online ta ruwaito.

Wannan na daga cikin shirin ba da tallafin karatu da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawo a farkon fara mulki.

Ba wannan ne karon farko ba, gwamnatin Kwankwaso, uban gidan Abba Kabir Yusuf ya sha ba da guraben karatu kyauta ga matasa a fadin jihar mai yawan jama'a.

Matakin da Abba ya dauka bayan tsige shi

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce ya sanar da lauyoyinsa da su garzaya zuwa kotun koli kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

A ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta yanke.

Kotun ta tsige Yusuf dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin gwamnan jihar Kano, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.