Mummunar Gobara Ta Lakume Kayayyakin Miliyoyin Nairori a Jihar Kwara
- An samu asarar miliyoyin nairori bayan wata mummunar gobara ta tashi a birnin Ilorin na jihar Kwara
- Mummunar gobara wacce ta tashi a rukunin wasu shaguna guda takwas ta laƙume kayayyakin da kuɗinsu sun kai N4.6m
- Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar ya bayyana cewa jami'an hukumar sun samu nasarar kashe gobara wacce ta tashi a dalilin tartsatsin wutar lantarki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta ce ta ceto shaguna guda shida da kayayyakin da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 68.5 a safiyar ranar Asabar, a wata gobara da ta tashi a titin yankin Basin a Ilorin, babban birnin jihar.
Gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe 2:06 na safe a titin Basin mai lamba 48 kusa da Cocin CAC dake ƙaramar hukumar Ilorin ta kudu ta ƙone wani rukunin shaguna guda takwas, cewar rahoton The Punch.
Mummunan gobarar dai ta tashi ne a dalilin tartsatsin wutar lantarki, a cewar sanarwar da shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, Hassan Adekunle ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tafka asara a dalilin gobarar
Adekunle, ya ce biyu ne kawai cikin shaguna takwas ɗin suka lalace saboda ɗaukin gaggawa da jami'an ƴan kwana-kwana suka kai, inda ya ce an yi asarar dukiyar Naira miliyan 4.6 a dalilin gobarar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
"Ma'aikatan kashe gobara sun bar ofishin su ba tare da ɓata lokaci ba, da isar su wurin, suka ci karo da wata mummunar gobara da ta lakume wani rukunin shaguna takwas, wacce ta yi sanadiyyar lalacewar biyu daga cikinsu." A cewarsa.
Ya ce ƴan kwana-kwana sun nuna kwarewa sosai kuma sun samu nasarar shawo kan gobarar da karfe 2:20 na dare.
Menene ya haddasa gobarar?
"Bincike na baya-bayan nan ya gano musabbabin lamarin a matsayin tartsatsin wutar lantarki." A cewarsa.
Sanarwar ta ƙara da cewa daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Falade John ya shawarci jama’a da su riƙa kashe na’urorin lantarki idan ba a amfani da su.
Gobara Ta Laƙume Wuraren Shaƙatawa
A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta laƙume wasu wuraren shaƙatawa guda huɗu a gefen asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase (MAWTH) a jihar Kano.
Gobarar wacce ta tashi sakamakon tartsatsin wutar lantarki ta lalata wuraren shaƙatawar gaba ɗaya.
Asali: Legit.ng