Bidiyon Yadda Fuskar Wata Mata Ta Sauya Gaba Daya Bayan Wani Ya Taba Ta a Wajen Birne Gawa

Bidiyon Yadda Fuskar Wata Mata Ta Sauya Gaba Daya Bayan Wani Ya Taba Ta a Wajen Birne Gawa

  • Labarin wata mata yar Najeriya, Franca Onyekaba, wacce fatarta ta kone, ya tsuma zukatan jama'a
  • Franka ta jaddada cewar ba shafe-shafen man bilicin bane yasa fatarta ta koma haka illa wani al'amari da ya faru a yayin bine yar'uwarta
  • Labarin mai karya zuciya yana tuni ga jama'a a kan su daina yanke hukunci da abun da idonsu ya gani maimakon haka su ji labarin mutum kafin su fara hasashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata dattijuwar mata yar Najeriya, Franca Onyekaba, ta yi fice bayan ta ba da labarin halin da ta shiga a wajen birne gawar yar'uwarta.

A wata hira tare da @jidekaijimedia a dandalin TikTok, ta magantu kan halin da fuskarta ke ciki da kuma abun da ya haddasa shi.

Kara karanta wannan

“Ba zan daina sonka ba”: Matashiya ta nunawa duniya saurayinta dan wada

Franca ta ce fuskarta ta sauya bayan wani ya taba ta
Bidiyon Yadda Fuskar Wata Mata Ta Sauya Gaba Daya Bayan Wani Ya Taba Ta a Wajen Birne Gawa Hoto: @jidekaijimedia/TikTok.
Asali: TikTok

Franca, wacce bata yi aure ba daga yankin Otolo Nnewi, ta ba da labarin abun da yasa take dauke da baki-baki a fuskarta, wanda ya yi sanadiyar da wasu da dama ke hasashen man bilicin ne ya lalata mata fuska.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Franca ta bayyana cewa ba man bilicin bane ya bata mata fuska

A cikin bidiyon mai taba zuciya, Franca ta fayyace cewa ba ita ta haifar da abun da ya same ta ba illa dai sanadin wani abu da ya faru a wajen jana'izar yar'uwarta.

A cewar matar wacce ta karaya, wani ne ya taba fuskarta yayin jana'izar kanwarta, wanda ya yi sanadiyar lalata fatar tata.

Bidiyon mai ban tausayi ya nanata muhimmancin kauracewa yanke hukunci da abun da ido ya gani.

An yi wa bidiyon take da:

"Labarinta akwai taba zuciya, har sai ka tattauna sosai da mutane, sannan ne za ka san abun da mutane ke fuskanta. Sunanta Franca Onyekaba daga Otolo Nnewi. Ka ajiye mata labaran karfafawa."

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya yi wa yan mata marayu 9 auren gata a jihar Zamfara, hotuna sun bayyana

Bidiyon matar da fuskarta ta lalace ya haifar da martani

Bidiyon na TikTok ya ja hankalin mutane da dama, lamarin da yasa labarin Franca ya yadu.

@Hanny ta yi martani:

"Bata da aure? Muryarta ta yi kama da wacce ke da kuruciya."

@kaka2 ta ce:

"Abubuwa na faruwa."

@Chi_bby2 ta ce:

"Abu makamancin wannan ya faru da yar'uwar kawata."

@chisaprincewill ta yi martani:

"Wannan ne abun da ya faru da mahaifiyata shekaru da dama da suka wuce. Har yau bamu san wanene ya yi mata ba."

@cuttielizy ta yi martani:

"Ba mai bane fa."

Matar da ta yi bilicin ta tuba

A wani labarin, mun ji cewa bidiyon wata mata wacce ta tuba ta daina yin bilicin ta koma kalar fatar jikinta ta ainihi, ya ɗauki hankula sosai.

Ɗiyar matar dai itace ta tambaye ta bayan ta ga hotunan aurenta inda ta lura da yadda kalar fatar jikinta tayi haske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng