Yanzu Yanzu: Kotun Daukaka Kara Na Shirin Yanke Hukunci a Karar Da Ke Neman Tsige Gwamnan APC
- Kotun daukaka kara ta fara zaman sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Lagas na 2023
- A yau laraba, 15 ga watan Nuwamba, ne kotun za ta yanke hukunci a kan shari'ar da ke neman a tsige Babajide Sanwo-Olu daga kujerar gwamnan Lagas
- Kwamitin kotun mai alkalai uku ya fara sauraron shari'ar da misalin karfe 3:06 na yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Lagos - Rahoto da ke zuwa mana ya tabbatar da cewar kotun daukaka kara na gab da yanke hukuncin karshe kan karar da ke neman a tsige Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas.
Daya daga cikin hadiman gwamnan, Jubril Gawat, ne ya tabbatar da ci gaban a cikin wani rubutu da ya yi a dandalin soshiyal midiya.
An tattaro cewa kwamitin kotun mai mutum uku da ke sauraron shari'ar, ya fara zama ne da misalin 3:06 na yamma.
Rubutun nasa na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Lagas na 2023 a yau...Shari'a na gudana a yanzu haka..kada ku matsa!!!"
Yan takarar LP da PDP ne suka daukaka kara zuwa kotun
Dan takarar gwamnan jam’iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour da takaransa na PDP, Abdulazeez Olajide Adedira, suna kalubalantar nasarar Sanwo-Olu na APC a zaben gwamnan jihar Lagas na 2023.
A ranar 25 ga watan Satumba, kotun sauraron kararrakin zabe ta kori kararrakin masu kalubalantar nasarar nasa sannan ta tabbatar da zaben Sanwo-Olu da mataimakinsa, Obafemi Hamzat.
Sai dai kuma, bayan hukunci, yan takarar sun garzaya kotun gaba domin ci gaba da kalubalantar nasarar tasa. Kuma duk hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben shine zai rufe shari'ar gaba daya.
Ana zaman dar-dar a Kano da Filato
A wani labari makamancin wannan kuma, mun ji cewa ana sa ran kotun daukaka kara za tayi hukunci a shari’o’in zaben Gwamnonin jihohin Filato da Kano kafin karshen mako.
Rahoton Daily Trust ya ce magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da mutanen Nasiru Yusuf Gawuna suna ta fatan samun nasara a kotun.
A baya kotun sauraron karar zaben Kano ta ce Nasir Yusuf Gawuna ne halataccen Gwamna da aka zaba, ta tsige Abba Kabir Yusuf da NNPP.
Asali: Legit.ng