Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Bankuna Su Ke Aiki a Lokacin Yajin Aiki

Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Bankuna Su Ke Aiki a Lokacin Yajin Aiki

  • Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya mayar da martani kan yajin aikin da kungiyar kwadago ta fara a faɗin ƙasar nan
  • Sani ya ce wasu bankunan kasuwanci ba su cika umarnin ƙungiyar ƙwadago wajen gudanar da yajin aikin
  • A cewar Sani, bankuna suna rufe ƙofofinsu na gaba amma suna umartar kwastomominsu da su yi amfani da ƙofar baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana yadda wasu bankunan kasuwanci suke gudanar da ayyukansu a lokacin yajin aikin da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Sani ya ce wasu bankunan suna rufe ƙofar shiga ta gaba ga kwastomominsu yayin da suke umartar kwastomominsu da su shiga ta ƙofar baya.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ribadu ya kira taron gaggawa da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, Bayanai Sun Fito

Shehu Sani ya yi magana kan yadda bankuna ke aiki a lokacin yajin aiki
Shehu Sani ya bayyana yadda bankuna ke gudanar da ayyukansu a lokacin yajin aiki Hoto: Shehu Sani/Eminent Media
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @Shehusani, a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sanatan ya yi mamakin ko rabin yajin aiki suke yi ne ko kuma wani abu daban.

"Wasu bankuna suna yajin aiki ta hanyar rufe kofar shiga da kuma gaya wa kwastominsu su shiga ta ƙofar baya, shin wannan rabin yajin aiki ne ko wani abu daban?"

Ƙungiyoyin ƙwadago sun tsunduma yajin aiki

Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar nan na har sai baba ta gani. Ƙungiyoyin ƙwadagon sun shiga yajin aikin ne kan dukan da aka lakaɗawa shugaban ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun umurci dukkanin ƙungiyoyin ma'aikata da ke ƙarƙashinsu, da su tsunduma yajin aikin, bisa umurnin majalisar zartaswa ta ƙungiyoyin.

Kara karanta wannan

To fa: Babbar matsala ta kunno kai, ta dakatar da sake gurfanar tsohon gwamnan CBN a Kotu

BUK Ta Dakatar da Jarrabawa Saboda Yajin Aiki

A wani labarin kuma, jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) ta dakatar da gudanar da jarrabawar zangon farko da ta ke yi saboda yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka tsunduma a faɗin ƙasar nan.

Jami'ar ta bayyana cewa hakan ya zama wajibi ne saboda bin umarnin da malaman jami'o'i suka yi na shiga cikin yajin aikin gama-garin da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng