Yanzu: Innalillahi, Wani Babban Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Wani Basaraken gargajiya a jihar Ogun, Oba Festus Oluwole Makinde, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 85 a duniya
- Rahotanni sun bayyana Sarkin ya rasu ne ranar Talata kuma fadarsa ta cika da masu zuwa jaje da ta'aziyya yau Laraba
- Wani matashi ɗan bautar kasa NYSC ya bayyana cewa an ɗage musu taron mako-mako saboda rasuwar basaraken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Sarkin gargajiya na garin Mowe a ƙaramar hukumar hukumar Obafemi Owode ta jihar Ogun, Oba Festus Oluwole Makinde, ya riga mu gidan gaskiya.
Basaraken wanda ake kira da Onigbein na Igbeinland ya mutu ne yana da shekaru 85 a duniya ranar Taata, 14 ga watan Nuwamba, 2023.
Wani matashi mai aikin bautar ƙasa watau NYSC, wanda ya nemi kada a ambaci sunansa, ya tabbatar da rasuwar Sarkin ga wakilin jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shaida wa jaridar cewa, Fadar marigayi Sarkin, wadda ta kasance wani ɓangaren ofishin NYSC na ƙaramar hukumar, ta cika makil da mutane masu zuwa ta'aziyya.
An ɗage taron CDS na NYSC saboda rasuwar
Matashin ɗan bautar ƙasan ya ce:
"Mun saba gudanar da taron mu na mako-mako amma yau aka sanar da mu babu taron wannan makon, daga baya muka fahimci cewa Sarki ne ya rasu jiya (Talata)."
Bayanai sun nuna an aje rijistar masu ta'aziyya a ƙofar shiga fadar saboda duk wanda ya zo ya rubuta sunansa.
Haka nan kuma jami'i mai kula da ofishin NYSC na ƙaramar hukumar, Dakta Oluyemisi Disu, ya sanar da sauya lokacin tantance masu hidima ga ƙasa na wata-wata saboda rasuwar Sarkin.
A wata sanarwa, ya ce:
"Sakamakon rasuwar Sarki, ba za a samu gudanar da taron CDS ba gobe Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023. Haka zalika ba za a buɗe Ofis ba sai ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba."
"Ga waɗanda ba a tantance su na wata ba, su nemi LGI a sansanin bada horo da ke Sagamu a jihar Ogun ranar Alhamis tsakanin ƙarfe 9-11:00 na safe."
Duk wani yunkuri na jin ta bakin fadar Sarkin kan wannan rashi ya ci tura har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton.
FG ta kama masu hannu a harin da aka kaiwa shugaban NLC
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta roki ƙungiyoyin kwadago su janje yajin aikin da suka fara kan abin da aka yi wa shugaban NLC a jihar Imo.
Mai ba da shawara kan tsaron kasa, Nuhu Ribaɗo, ya ce an kama waɗanda suka farmaki Ajaero kuma bincike ya yi nisa.
Asali: Legit.ng