Yajin Aiki: Abu Ya Girmama, Ma'aikata Sun Sha Mamaki Yayin da Suka Fita Wurin Aiki a Jihar Arewa

Yajin Aiki: Abu Ya Girmama, Ma'aikata Sun Sha Mamaki Yayin da Suka Fita Wurin Aiki a Jihar Arewa

  • Kungiyar ma'aikatan Najeriya ta hana ma'aikatan jihar Filato da na tarayya shiga wuraren aikinsu ranar Talata a Jos
  • Ma'aikatan sun ga abin mamaki yayin da suka tarad da mambobin NLC sun kewaye ofisoshinsu, sun basu umarnin su koma gida
  • Wannan na zuwa ne yayin da NLC da TUC suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a faɗin Najeriya

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Ma'aikatan Gwamnatin jiha da na tarayya da suka fita wuraren aiki ranar Talata a jihar Filato, sun ga abin da wataƙila ba su yi tsammani ba.

NLC ta rufe sakateriyar gwamnatin tarayya da ta jihar Filato.
Yajin Aiki: Abu Ya Girmama, Ma'aikata Sun Sha Mamaki Yayin da Suka Fita Wurin Aiki a Jihar Arewa Hoto: NLC
Asali: Depositphotos

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ma'aikatan sun taras da ma'aikatun da suke aiki a kulle, an datse ƙofofin shiga da kwaɗo da makulli.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar Gwamnatin jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna tare da sace mutane

Wasu daga cikin mambobin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) da suka datse kofofin shiga ma'aikatun, sun umarci ma'aikata su koma gida tun 12:00 na safe aka fara yajin aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A babbar Sakateriyar Gwamnatin jihar Filato, ma'aikata sun juya zuwa gida ba shiri yayin da suka tarad da mambobin kungiyar kwadago sun datse kofar shiga.

Makamancin haka ne ya faru a Sakateriyar Gwamnatin tarayya mai nisan mita 300 daga Sakateriyar jiha, dole ma'aikata suka juya zuwa gidajensu.

Bankuna sun bi sahu a Jos

Haka ne ke faruwa a ɓangaren bankunan kasuwanci da ke cikin Jos, babban birnin jihar Filato, mafi akasari sun kulle, sun hana kwastomomi shiga.

Wasu ma'aikatan banki duk da haka sun nemi a ba su damar gudanar da ayyuka kaɗan-kaɗan na yau kaɗai, amma daga gobe zasu bi sahun shiga yajin aikin gadan-gadan.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Shugaba Tinubu Ya Fusata, Ya Ce Matakin ‘Yan kwadago Ya Sabawa Doka

Wasu daga cikin jagororin NLC a kofar Sakayariyar tarayya sun ƙi yarda su ce wani abu kan wannan lamari, inda suka bayyana cewa shugabanni jiha ne ke da ikon magana da ƴan jarida.

Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Gagarumin Mataki

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta kira taron tattaunawa da kungiyar kwadago don dakatar da yajin aikin gama gari da ke gudana.

Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong, ya dauki matakin a daren ranar Litinin bayan kungiyar kwadago ta kaddamar da yajin aikin gama gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262