Direban da Ya Murkushe ’Yan Mata Masu Sharan Titi Har Lahira Ya Mika Wuya, an Fadi Hukuncinsa

Direban da Ya Murkushe ’Yan Mata Masu Sharan Titi Har Lahira Ya Mika Wuya, an Fadi Hukuncinsa

  • A daren jiya Litinin direban motar da ya murkushe ‘yan mata masu sharan titi a Legas ya mika kansa ga jami’an ‘yan sanda
  • Direban ya mika kansa ne a daren jiya Litinin 14 ga watan Nuwamba ga ‘yan sanda bayan markade masu sharan a jiya Litinin 13 ga watan Nuwamba
  • Wannan na zuwa bayan direban motar ‘Honda Saloon’ ya yi ajalin masu sharan titi biyu mata ‘yan gida daya a Legas a jiya Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – A karshe, direban motar da ya murkushe ‘yan mata masu sharan titi ya mika kansa ga jam’ian ‘yan sanda.

Direban ya mika kansa ne a jiya Litinin 13 ga watan Nuwamba ga ‘yan sanda bayan markade masu sharan a jiya Litinin 13 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tinubu ya bada umurnin janye 'yan sanda masu tsaron manyan mutane

Direaban da ya yi ajalin masu sharan titi ya mika kansa
'Yan sanda sun tabbatar da cewa direban ya mika kansa. Hoto: LASTMA.
Asali: Facebook

Mene direban ya aikata a Legas?

Legit Hausa ta ruwaito a jiya cewa direban ya yi ajalin matan ne yayin da ya ke kokarin kaucewa kamun jami’an LASTMA a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan take matan guda biyun wadanda ‘yan gida daya ne suka ce ga garinku a kan hanyar Gbagada a Legas.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Legas, SP Benjamin Hundeyin shi ya bayyana haka a yau Talata 14 ga watan Nuwamba, cewar Channels TV.

Mene ‘yan sanda suka ce a Legas?

Hundeyin ya tabbatar wa Punch cewa direban ya mika kansa a daren jiya inda ya ce za a tasa keyarshi zuwa kotu don yanke hukunci.

Ya ce:

“Direban mota kirar ‘Honda Saloon’ ya mika kansa a jiya Litinin da dare kuma za a gurfanar da shi a kotu,
“Saboda ba da gan-gan ya aikata kisan ba, ta zo ne da tsautsayi don haka zai samu sassauci a shari’ar.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bai wa asibiti gudunmawar naira miliyan 20, ya bayyana dalili

Har ila yau, Ma’aikatar Sufuri a jihar a daren jiya Litinin 13 ga watan Nuwamba ta musanta zargin akwai hannun jami’in LASTMA a kisan, cewar The Nation.

Mota ta murkushe masu sharan titi

Kun ji cewa, wani direban mota ya yi ajalin masu sharan titi a Legas a kokarin kauce wa kamun jami’an LASTMA.

Wadanda abin ya shafa ‘yan mata ne guda biyu inda aka tabbatar cewa ‘yan gida daya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.