Abin Tausayi Yayin da Direba Ya Murkushe Masu Sharan Titi 2 a Kokarin Kauce Wa Kamun Jami'an LASTMA
- Mata biyu sun rasa rayuwarsu yayin da su ke sharan titi a jihar Legas da safiyar yau Litinin
- Matan sun rasa ransu ne bayan wani direba ya doke su har lahira a kokarin guje wa kamun jami'an LASTMA
- Shaidun gani da ido sun ce matan 'yan gida daya ne da suke aikin share titunan kafin wannan iftila'i ya afka musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Wasu masu sharan titi mata biyu sun gamu da ajalinsu bayan direban mota ya murkushe su a jihar Legas.
Matan biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin da direban ke kokarin tserewa jami'an kula da hanya ta LASTMA da ke Legas a kan hanyar Oshodi zuwa Gbagada.
Mene sanadin mutuwar masu sharan titin a Legas?
An gano gawarwakin masu sharan a cikin kwalbati yayin da jama'a ke nuna alhinin mutuwarsu, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faruwar lamarin ya jawo cikas ga masu ababan hawa da ke wuce wa yayin da jama'a suka cika wurin da abin ya faru.
Shaidun gani da ido sun bayyana wa Daily Trust cewa wadanda suka mutun 'yan gida daya ne da suke aikin share tituna a birnin.
Mene martanin hukumar LAWMA a Legas kan mutuwar?
Ya ce:
"Wannan rashin imani kullum karuwa yake yi, gwamnatin jihar da hukumar LASTMA su na cin zarafin mutane ya kamata a dauki mataki."
"Dubi abin da ya faru 'yan gida daya sun mutu saboda jami'an LASTMA na bin wata mota, wannan abin ya dade ya na faruwa."
Da ta ke martani, Hukumar Tsaftace Muhalli a Legas LAWMA, ta nuna damuwarta kan mutuwar ma'aikatanta inda ta ce abin takaici ne.
Mata ta mutu yayin raba fada a cikin coci
A wani labarin, wata mata ta rasa ranta yayin da take kokarin shiga tsakanin masu fada a cikin coci a jihar Legas.
Matar mai shekaru 47 ta rasa ranta ne bayan ta yi kokarin raba fadar a cocin yayin da wani ya soka mata abu mai kaifi da ya yi ajalinta.
Asali: Legit.ng