Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Hukumar INEC Ta Sanar Da Ceto Ma'aikaciyarta da Aka Sace
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ƙasa (INEC) ta sanar da ƙuɓutar da ma'aikaciyarta da aka sace ana gobe zaɓen jihar Bayelsa
- Hukumar ta sanar da cewa Ebehireme Blessing Ekwe ta kuɓuta ne bayan an sace ta a ranar Asabar, 10 ga watan Nuwamba
- Hukumar INEC ta sanar da kuɓutar da Ebehireme ne a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter)
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Yenagoa, jihar Bayelsa - An sako jami’ar sa ido kan zaɓe (SPO) da aka sace, Ebehireme Blessing Ekwe, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
An yi garkuwa da Ekwe ne a ranar Juma’a, 10 ga watan Nuwamba, a jajibirin zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @inecnigeria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar na cewa:
"Hukumar INEC na farin cikin sanar da cewa an kuɓutar da jami’ar sa ido ta hukumar, Ms Ebehireme Blessing Ekwe, wadda aka yi garkuwa da ita a jajibirin zaɓen gwamnan jihar Bayelsa."
"A cikin hoton da aka maƙala: Ebehireme (tsakiya) na tare da ƙwamishiniyar zaɓe ta ƙasa mai kula da Jihar Bayelsa, Misis May Agbamuche-Mbu (a hagu) da kwamishinan ɓabe na jihar, Mista Obo Effanga.”
Gwamna Diri ya lashe ƙaramar hukuma ta farko
Gwamnan jihar Bayelsa Duoye Diri da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun samu nasara mai tazara a ƙaramar hukumar farko bayan an fara tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Gwamna Diri ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Timipre Sylva a ƙaramar hukumar Koluma/Opokuma, da tazarar sama da ƙuri'u dubu 10,000.
Gwamnan wanda ya fito daga ƙaramar hukumar ya samu ƙuri'u 18,465, sai Sylva ya samu ƙuri'u 5,349, sai ɗan takarar jam'iyyar LP da ya samu ƙuri'u 22.
Asali: Legit.ng