Wata Mata Ta Yada Bidiyon Wani Halitta da Ta Gani a Dakinta, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wata Mata Ta Yada Bidiyon Wani Halitta da Ta Gani a Dakinta, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • A wani bidiyon TikTok mai ban mamaki, wata mai suna @pethealer1225 ta nadi wani abun al'ajabi da ta ci karo da shi
  • Kamar yadda mai amfani da TikTok din ta bayyana, wani dabba da bata san ko menene ba ya bayyana a gidanta da daddare kuma ya haddasa yar dirama
  • Lamarin ya jefa mutane da dama a rudu yayin da suke iya bakin kokarinsu don gano kowani irin halitta ne wannan

Wata mai amfani da TikTok mai suna @pethealer1225 ta yada wani bidiyo da ke nuna arangamar da ta yi da wani irin dabba da bata san ko menene ba.

Dabban mai ban mamaki ya samu shiga cikin gidanta da daddare ba tare da kowa ya ci karo da shi ba.

Wata mata ta ci karo da wani dabba a gidanta
Matar da ke hoton bata da alaka da labarin, an yi misali da ita ne Hoto: @pethealer1225/TikTok, ROBERTO SCHMIDT/ Getty Images.
Asali: UGC

Dirama yayin da wani dabba ya shiga gidan wata mata

Kara karanta wannan

Wata mata da ta auri miji dan tsurut ta baje kolin cikinta, ta haifo santaleliyar jaririya

Wannan bidiyo ya baje kolin lamarin mai rudarwa, inda ya bar masu kallo cikin zullumi game da inda wannan halitta da tushensa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dabban da ke da launin ruwan kasa a jikinsa da idanu masu duhun gaske ya rataye a saman wata doguwar taga sannan ya zubawa mai gidan idanu yana kallonta.

Jama'a sun yi martani kan bidiyon dabba mai ban mamaki

@Luna Zee ta yi martani:

“Dabban 'Slow loris', yana da tsananin kyau amma yana da dafi."

@FawnSilva ta ce:

"Wannan dabban 'Slow Loris' ne basa fitowa da rana.

@nana ta ce:

"Yanzu a wace duniya kike zaune da kika samu dabban 'Slow Loris' a dakinki."

@Skitten Says ta yi martani:

"Me yasa aka samu dabban 'Slow Loris' a gidanki???"

@joyoussss_ ta ce:

"A ina kike da har kika samu wannan a cikin gidanki??"

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

@Moriah St. Louis ta ce:

"Bana jin dadi kwata-kwata bayan na bincika 'solpw loris' a intanet."

Kalli bidiyon a kasa:

Akuya ta cusa kai cikin butan karfe

A wani labari na daban, mun ji cewa an yi nasarar ceto wata akuya da kanta ya makale a cikin wani buta bayan makwabta sun taru a wajen.

A cikin wani bidiyo mai ban dariya da ya yadu a soshiyal midiya, alamu sun nuna akuyar tana neman abun sakawa a baki a cikin butan.

Ta taki rashin sa'a yayin da kanta ya makale a cikin butan, sannan ta dungi fama wajen numfasawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng