‘Ku Yi Hakuri’, MTN Ya Yi Martani Kan Yafe Basukan a Layukan Jama’a, Ya Fadi Dalili

‘Ku Yi Hakuri’, MTN Ya Yi Martani Kan Yafe Basukan a Layukan Jama’a, Ya Fadi Dalili

  • Kamfanin MTN ya yi martani kan yafe basuka da masu amfani da layuka suka fuskanta a yau
  • An wayi garin yau Asabar da samun sakwannin cewa kamfanin ya kwashe dukkan basukan jama'a
  • Mutane sun yi ta murna da ganin haka kafin daga bisani kamfanin ya fitar da sanarwa kan matsalar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Masu amfani da layukan kamfanin MTN sun wayi garin yau da murna yayin da aka yafe musu dukkan basukansu.

A yau Asabar 11 ga watan Nuwamba, an yi ta tura wa mutane sakon cewa an yafe musu basukan da ke cikin layikansu, Legit ta tattaro.

Kamfanin MTN ya yi martani kan yafe basukan kwastomomi a Najeriya
MTN ya yi magana kan yafe basukan masu amfani da layukanshi. Hoto: George Osodi.
Asali: Facebook

Wane dama MTN ke bai wa kwastomominsa?

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Kamfanin MTN ya na bai wa kwastomomi damar cin bashi idan kudaden kirarsu ta kare yayin da suke bukatar kira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke karin haske ga Legit, babban manajan hulda da jama’a na kamfanin, Fusho Aina ya tabbatar da lamarin.

Har ila yau, Aina ya ce wannan matsalar na’ura ce ta jawo aka kwashe dukkan basukan da ake bin jama’a.

Wane martani kamfanin MTN ya yi?

A cikin sanarwar da MTN ya fitar ta ce:

“MTN Najeriya ta tabbatar da matsalar na’ura yayin duba sauran kudade a wayoyin ku.
“A dalilin haka, wasu daga cikin kwastomomi sun samun sakon cewa an yafe musu basukan da ake binsu.
“Da zarar an kamala shawo kan matsalar, basukan za su dawo, injiniyoyinmu suna kan gyara don shawo kan matsalar, muna baku hakuri.”

‘Yan Najeriya da dama sun yi farin ciki ganin yadda aka yafe musu basukan kafin daga bisani su shiga yanayi bayan sanarwar kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.