Zaben Gwamnan Kogi Na 2023: Dino Melaye Ya Nemi a Soke Zabe a Kananan Hukumomi 5
- Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar Kogi ya koka kan yadda aka gudanar da zabe a yankin Kogi ta tsakiya
- Dino ya bukaci hukumar zabe da ta soke zabe a kananan hukumomi biyar na yankin
- A cewar tsohon dan majalisar, an tafka magudi a kananan hukumomin Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta soke zabe a kananan hukumomi biyar na jihar.
Melaye ya ce zaben da aka gudanar a wadannan yankuna na cike da magudi na fitar hankali.
Tsohon dan majalisar tarayyar ya lissafa kananan hukumomin da yake son a soke zabe a matsayin Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo – gaba dayansu a yankin Kogi ta tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi kiran ne a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @_dinomelaye
"Ya zama dole INEC ta soke zabe a kananan hukumomi 5 na Kogi ta tsakiya. Zaben da aka yi a Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo duk suna cike da zamba na fitar hankali."
Dino Melaye ya lashe rumfarsa
A wani labarin, mun ji cewa Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu nasarar lashe rumfar zaɓen da yake kaɗa kuri'a.
Tsohon mamban majalisar dattawan ya lallasa jam'iyyar APC da gagarumin rinjaye a rumfar zaɓensa da ke Iluafon quarters, RA: Aiyetoro 1, ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi.
Sanata Melaye ya samu ƙuri'u 210 a zaben da aka kaɗa yau Asabar a rumfar zaɓen inda ya lalllasa babban abokin adawarsa na jam'iyyar APC, Usman Ododo, wanda ya samu kuri'u 22.
Asali: Legit.ng