An Sace Jami'in INEC, Takardar Sakamakon Zabe Sun Bace a Hatsarin Jirgin Ruwa a Bayelsa
- Rahotanni sun bayyana cewa an sace jami'in zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa zai yi aikin zabe a karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa
- Haka zalika, hukumar zaben ta sanar da cewa wasu jami'anta sun yi hatsarin jirgin ruwa, wanda ya yi sanadin bacewar takardar rubuta sakamakon zabe
- Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar za ta gudana da zaben gwamna a jihar, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Bayelsa - An yi garkuwa da jami’in sa ido ga jami'an zabe (SPO) na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da aka tura gundumar zabe mai lamba 06 a garin Ossioma da ke karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa.
Jami’in na INEC, wanda ba a gano sunan sa a lokacin da ake tattara wannan rahoto,, an ce an yi garkuwa da shi ne a unguwar Amassoma da ke Kudancin karamar hukumar Ijaw, a lokacin da yake jiran ya hau jirgin ruwa, a wata tashar jirgin da ke yankin.
Haka zalika, wani jirgin ruwa dauke da jami’an zabe zuwa gudumar zabe ta 17 a yankin Koluama da ke karamar hukumar Ijaw ta Kudu, ya kife da kayayyakin zabe, ciki har da takardar rubuta sakamakon zabe, wadanda aka gagara gano su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mun yi asarar kayyakin zabe a Bayelsa - INEC
Shugaban sashen Ilimantar wa da wayar da kan masu kada kuri’a na INEC, a jihar Bayelsa, Mista Wilfred Ifogah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ba a yi asarar rayuka ba.
Ya kara da cewa, an ceto ma’aikata 12 tare da matukin jirgin ruwan.
Yace:
“Muna so mu tabbatar da cewa, wani jirgin ruwa dauke da ma’aikata zuwa yankin gundumar zabe ta 17 (Koluama), a Kudancin karamar hukumar Ijaw ya kife, an yi sa’a, ba a samu asarar rai ba, domin an ceto dukkan jami’an zabe 12 da ma’aikacin jirgin.
“Sai dai mun yi asarar takardun rubuta sakamakon zabe, na'urorin ba da wutar lantarki da jakunkuna masu dauke da kayayyakin amfanin ma’aikatan."
Hukumar 'yan sanda ba ta ce komai game da rahoton INEC ba
Game da rahoton sace ma'aikacin hukumar zaben, Ifogah ya ce:
“INEC, ta kuma bayar da rahoton cewa an sace SPO din ta da ke yankin mazaba mai lamba 06 (Ossioma), a karamar hukumar Sagbama, a lokacin da yake kokarin hawa jirgin ruwa, a Amassoma. An sanar da hukumomin tsaro kan faruwar lamarin"
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, CSP Asinim Butswat, bai ce komai ba game da lamarin ba, kawo zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto, domin bai dauki waya ko amsa sakonni ba.
Bayelsa 2023: Jerin sunayen yan takara 16 da jam’iyyunsu
Kun ji cewa, a jihar Bayelsa, yan takara da jam'iyyun siyasa 15 ne za su fafata da Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP a zaben gwamna na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, Legit Hausa ta ruwaito.
Manyan abokan hamayyar Diri sune tsohon gwamna kuma tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva na APC da Udengmobofa Eradiri na LP, da kuma wasu 13. Za su fafata da gwamnan a ranar Asabar don sanin shugaban jihar na gaba.
Asali: Legit.ng