'Yan Sanda Sun Tarwatsa Mata da Barkonon Tsohuwa Kan Abu Daya Tak, Sun Fadi Dalili
- Rundunar 'yan sanda ta dauki mataki kan ma su zanga-zangar cire kwamishinan 'yan sanda a jihar Bayelsa
- 'Yan sandan sun tarwatsa matan da ke zanga-zangar da barkonon tsohuwa bayan sun ki bin umarnin rundunar
- Matan sun bukaci sifetan 'yan sanda da Shugaba Tinubu da su umarci sauke Tolani Alausa saboda ba za a yi adalci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Rundunar 'yan sanda ta tarwatsa wasu mata da ke zanga-zangar dole a cire kwamishinan 'yan sanda a jihar Bayelsa.
Matan sun durfafi hedikwatar 'yan sandan da ke Yenagoa babban birnin jihar kan a cire kwamishinan 'yan sanda Tolani Alausa daga mukaminsa.
Mene dalilin zanga-zangar a Bayelsa?
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar, cewar Intel Region.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matan sun yi zanga-zangar ne a yau Juma'a 10 ga watan Nuwamba inda su ke zargin Alusa ba zai yi adalci ba a zaben da za a gudanar a gobe.
Matan sun yi shigar nuna alhini da bakaken kaya inda su ka bukaci Sifetan 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun da ya dauki mataki.
Wane kira matan su ka yi a Bayelsa?
Sun kuma kirayi Shugaba Tinubu da ya ba da umarnin cire kwamishinan don samun adalci a yayin zaben, cewar TheCable.
Daga bisani 'yan sanda sun tarwatsa su da barkonon tsohuwa yayin da su ka ki bin umarnin rundunar na barin wurin idan ba a biya mu su bukatarsu ba.
An nada Alausa mukamin kwamishina a ranar 7 ga watan Nuwamba wanda shi ne kwamishina na 36 a jihar.
Gwamna Diri ya ce shi zai yi nasara
A wani labarin, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya ce ya na da tabbacin shi zai lashe zaben da za a gudanar a gobe Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Diri ya bayyana haka ne yayin kamfe dinsa inda ya ce irin ayyukan alkairi da ya shimfida sun isa ba shi nasara a zaben da za a gudanar.
Asali: Legit.ng