Malamin Addini Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Ya Kamata CBN Ta Dakatar Da Amfani Da Sabbin Kudi

Malamin Addini Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Ya Kamata CBN Ta Dakatar Da Amfani Da Sabbin Kudi

  • Babban malamin addinin kirista, Elijah Ayodele ya yi kira da a janye sabbin takardun naira na Najeriya, inda ya bayyana su a matsayin “shaidanun kudade”
  • Malamin ya bukaci gwamnan CBN, Yemi Cardoso, da ya ba da umurnin amfani da tsofaffin takardun kudi kawai, yana mai cewa sabbin kudin "farar kafa ne"
  • Bugu da kari, Ayodele ya yi hasashen cewa Cardoso zai fuskanci kalubale daga 'yan siyasa da kuma bankuna a lokacin shugabancinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas, Najeriya - Babban fasto, Elijah Ayodele, ya shawarci gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, da ya janye sabbin takardun naira daga hannun jama'a.

Shugaban Cocin INRI Evangelical Spiritual ya bayar da wannan shawarar ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

Primate Ayodele, babban bankin Najeriya
Primate Ayodele ya ce sabbin takardun kudin za su jawo babbar asara a Najeriya Hoto: @DrYemiCardoso, @Nwaadaz, @primate_ayodele
Asali: Twitter

Sabbin takardun naira za su jawo asara, in ji Ayodele

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar malamin, kara buga sabbin takardun kudi zai jefa Najeriya cikin babbar asara, wanda za a iya kaucewa ta hanyar daina amfani da su kawai.

Primate Ayodele ya ce tsaffin takardun kudin ne suka fi dacewa da Najeriya kuma ya kamata su zama kudi tilo da za a rinka amfani da su a kasar.

A cewar sa:

"Ya kamata Gwamnan CBN ya janye sabbin takardun kudi da tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya kawo. Sabbin kudin za su jawo babban asara."

Abin da ke jiran gwamnan CBN, Cardoso - Fatawar Ayodele

Haka zalika, fasto Ayodele ya kuma fitar da wata fatawa game da shugabancin sabon gwamnan CBN da aka nada, Cardoso.

Ya ce shugaban na CBN zai yi garambawul amma zai samu matsala da ‘yan siyasa da kuma bankuna, kamar yadda ya gargade shi da wasu tsare-tsare da za su shafi nasarar sa.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Mun Shirya Buga Isassun Sabbin Kudi: Kamfanin NSPM

A wani labarin, kunji kamfanin buga kudin Najeriya (NSPM) ya bayyana cewa ya gama shirye-shiryen cigaba da buga sabbin kudin Najeriya da aka sauya wa fasali.

Wannan ya biyo bayan labarin da ke yawo na cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana rashin isassun kayan aikin buga kudaden a masana'antar NSPM, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.